Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa babban Sarkin Gargajiya wuta, sun kashe shi
- Yan awanni bayan Sarkin Musulmi yayi magana da hare-haren yan bindiga, an dau ran wani sarkin gargajiya
- Har yanzu hukumar yan sanda ba tayi tsokaci kan lamarin ba
Yan bindiga sun kashe Olufon of Ifon, Oba Isreal Adeusi, a karamar hukumar Ose na jihar Ondo a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, 2020.
Rahoton The Punch ya nuna cewa Oba Adeusi na kan hanyar komawa gida daga wata ganawa a Akure misalin karfe 4 yayinda wasu yan bindiga suka bude masa wuta.
Majiyoyi sun bayyana cewa shi kadai aka kashe a harin kuma babu abinda aka sata.
An samu labarin cewa an ajiye gawarsa a asibitin FMC.
Dan'uwar sarkin ya bayyanawa Punch cewa, "Yana kan hanyar dawowarsa mai lamba ta musamman. ya tafi Akura wata ganawa. Amma a hanyar dawowarsa kusa da wata hanya da tayi kaurin suna wajen Elegbeka, an tare shi kuma aka bindigeshi."
"Tabbas an tafi kasheshi ne saboda babu abinda aka sace a cikin motar kuma babu abinda ya samu sauran mutanen dake motan."
KU KARANTA: Ganduje: Na biya N1.8bn kan daliban da Kwankwaso ya yi watsi da su
A wani labarin kuwa, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar II, ya yi Alla-wadai da lamarin tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya, inda yace yan bindiga na cin karansu ba babbaka.
Sarkin Musulmi wanda shine shugaban majalisar koli ta lamuran addini a Najeriya ya bayyana cewa yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna awon gaba da mutane a Arewa.
Alhaji Sa'ad ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin taron majalisar hadin kan addinai NIREC da akayi a Abuja.
KU KARANTA: Hukumar Soji ta karawa marigayi Kanal Bako girma zuwa Birgediya Janar don karramashi
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng