Cikin kwanakin nan za mu kawo karshen ta'addanci, Hedkwatar tsaro

Cikin kwanakin nan za mu kawo karshen ta'addanci, Hedkwatar tsaro

- Kwanan nan ta'addanci zai zo karshe a Najeriya, cewar kakakin rundunar sojin Najeriya, John Enenche

- Ya fadi hakan ne a ranar Alhamis, yayin gabatar da jawabi game da nasarorin sojoji a Abuja

- A cewarsa, a ranar 21 ga watan Nuwamba, rundunar soji ta ragargaji 'yan ta'addan arewa maso yamma

Hedkwatar tsaro ta tabbatar da yadda kwanan nan za ta kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin taron bayar da bayani a kan ayyukan rundunar soji.

A cewarsa, ta yadda sojoji suke ragargazar 'yan ta'adda, kwanan nan za su zama tarihi.

Ya kara da cewa: "Rundunar Operation Hadarin Daji da sauran rundunoni masu taimakonsu suna ragargazar 'yan ta'addan arewa maso yammacin kasar nan kuma suna samun nasarori na ban mamaki.

KU KARANTA: 2023: Mulkin karba-karba ba zai shawo kan matsalolin Najeriya ba, El-Rufai

Cikin kwanakin nan za mu kawo karshen ta'addanci, Hedkwatar tsaro
Cikin kwanakin nan za mu kawo karshen ta'addanci, Hedkwatar tsaro. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buni ga Sanatocin APC: Ku zage damtse, nasara tamu ce a kodayaushe

"Jaruman sojojin suna ratsa dazuzzuka, lungu da sako wurin neman 'yan ta'adda a maboyarsu.

"A ranar 21 ga watan Nuwamban 2020, rundunar Operation Accord sun samu nasarar kashe 'yan bindiga 2 har suka samo bindigogi kirar AK47 guda 2.

"Sannan a ranar 21 ga watan Nuwamban 2020, rundunar ta je sintiri wuraren kauyen Gobirawa suka yi kacibus da 'yan bindigan. A karon battar, sun kashe 'yan bindiga 6, sannan suka samu bindigogi 2 kirar AK 47, kananun bindigogi 3 da babura 2.

"Sannan bayan rundunar sun yi amfani da dabara ta musamman, sun gano wasu mutane masu hako ma'adanai ba bisa ka'ida ba guda 11.

"Rundunar sun tura duk wadanda ake zargin ofishin 'yan sanda don a cigaba da bincikarsu."

A wani labari na daban, wasu miyagu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai hari yankin Yolde pete da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.

Mazauna yankin tare da jami'an tsaro sun tabbatar da cewa, miyagun dauke da makamai sun tsinkayi gidan dansanda makusancin Atiku Abubakar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
NDA