'Yan bindiga: SSS sun damke mata da miji dauke da harsasai a Katsina

'Yan bindiga: SSS sun damke mata da miji dauke da harsasai a Katsina

- Jami'an 'yan sandan farin kaya sun kama wani Usman Shehu da matarsa, Aisha Abubakar da miyagun kaya

- Sun kama su ne a wani kauye da ke karamar hukumar Rimi a jihar Katsina, a ranar 22 ga watan Nuwamba

- Kakakin rundunar soji, John Enenche ya sanar da hakan a ranar Alhamis a wani taro na sojoji a Abuja

Jami'an tsaro na farin kaya na jihar Katsina sun damki wani miji da matarsa da miyagun makamai. Ana zargin Usman Shehu da matarsa Aisha Abubakar da ta'addanci.

Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taron da sojoji suka yi.

A cewarsa, an kama wadanda ake zargin a kauyen Abukur da carbi 14, caliber ammunition rounds 61 na 9.6mm da special ammunition rounds 399 na 7.62mm.

KU KARANTA: 2023: Mulkin karba-karba ba zai shawo kan matsalolin Najeriya ba, El-Rufai

'Yan bindiga: SSS sun damke mata da miji dauke da harsasai a Katsina
'Yan bindiga: SSS sun damke mata da miji dauke da harsasai a Katsina. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

A cewarsa: "Rundunar soji sun kara samun wata nasara a ranar 22 ga Nuwamban 2020, inda 'yan sanda masu fararen kaya na jihar Katsina suka damki wani Usman Shehu da matarsa Aisha Abubakar, a karamar hukumar Rimi da ke jihar Katsina.

"Jami'an tsaron sun yi kacibus da 'yan ta'addan a daidai kauyen Abukur, suna dauke da miyagun makamai masu dumbin yawa. An kama su da magazines 14, rounds 61 na 9.6mm caliber ammunition da rounds 399 na 7.62mm special ammunition."

KU KARANTA: EFCC ta bayyana wani fitacce da suka hada kai da Maina wurin wawure kudin fansho

A wani labari na daban, jam'iyyar APC ta jihar Legas ta fara fuskantar rabuwar kawuna cikin manyan 'yan jam'iyyar. Olajide Adeniran, ya zargi gwamnatin jihar ta yanzu da damawa da mutane kalilan.

A wani taro da suka yi a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba, inda ya sanar da burinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar da zarar Babajide Sanwo-Olu ya sauka, kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel