Bidiyon amarya tana cashewa cike da gwaninta a liyafar bikinta ya janyo cece-kuce

Bidiyon amarya tana cashewa cike da gwaninta a liyafar bikinta ya janyo cece-kuce

- Wata amarya 'yar Najeriya ta baje kolinta a ranar aurenta

- Chimdi ta tafi tsakiyar fili ta kwashi rawarta cikin kwarewa

- Angon tsayawa kawai yayi a gefe yana kallon ikon Allah

Bidiyon wata amarya 'yar Najeriya mai suna Igwe Etomchi Chimdi da angonta ya karade kafafen sada zumuntar zamani. Mutane da damu sun yi ta magana a kan zakewar amaryar wurin cashewa da rawa.

Bidiyon, wanda Legit.ng ta gani a kafar sada zumuntar zamani na Instagram, ya nuna wata amarya da angonta, tsaka da shagalin bikinsu na gargajiya, suna sanye da sitturu masu kalar ja da fari, sannan baki sun zagayesu.

Amarya da angon sun yi ta kwasar rawa har sai da DJ ya sanya wata waka mai suna Skeleton Move, wacce Master KG ya rera.

KU KARANTA: Bidiyon soji suna ragargaza 'yan bindiga a dazuzzukan Birnin Kogo daga Ajjah

Bidiyon amarya tana cashewa cike da gwaninta a liyafar bikinta ya janyo cece-kuce
Bidiyon amarya tana cashewa cike da gwaninta a liyafar bikinta ya janyo cece-kuce. Hoto daga @tomsybabe
Asali: Instagram

KU KARANTA: Gwamonin Kudu: Ma'adanan yankinmu ake amfani da su amma an bar mu cikin mawuyacin hali

Amaryar ta dage wurin nuna bajimtar ta, duk da tana daure da zani, amma hakan bai dakatar da ita ba. Har sai da angon ya matsa gefe ya zubawa sarautar Allah ido.

Angon ya ga irin zakewar da amaryar tayi, sai ya daura hannunsa a kugunsa, yana kallon rawan yana gyada kai.

A wani labari na daban, 'yan uwa da abokan arzikin Theresa Yohanna Bwai, mai shekaru 52 da danta, Bweifar Isaac, mai shekaru 22, suna cikin matsanancin tashin hankali.

Matar ta fadi ta mutu bayan ta samu labarin mutuwar danta daya tal a jihar Filato, shafin Linda Ikeji ya bayyana hakan.

Kamar yadda bayanai suka kammala, wasu 'yan ta'adda sun harbi Isaac, mai shekaru 22, wanda mawaki ne, mai daukar hoto kuma dalibi ne a jihar Jos, ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba da daddare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel