Dakarun soji sun tarwatsa sansanin 'yan bindiga a iyakar Kaduna da Niger

Dakarun soji sun tarwatsa sansanin 'yan bindiga a iyakar Kaduna da Niger

- Rundunar sojin sama ta ritsa wasu 'yan bindiga wuraren iyakar Kaduna da jihar Neja

- Sojojin sun je sintiri wuraren Kawuri, ba su yi kasa a guiwa ba suka yi biji-biji da 'yan ta'addan

- Sun tarar 'yan ta'addan sun banka wuta a gidaje da wuraren bautar mutanen yankin

Rundunar sojin sama ta yi kaca-kaca da wasu 'yan ta'adda a karamar hukumar Chukun, kusa da iyakar jihar Neja.

A ranar Laraba da safe, jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan ta'adda suka kai wa wuraren Kugosi da Kajari da ke cikin karamar hukumar Chikun hari.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya sanar da hakan a wata takarda ta ranar Alhamis, inda yace gwamnatin jihar ta yi gaggawar tuntubar sojoji wadanda suka tabbatar musu da sun tura wata runduna don ta ragargaji 'yan bindigan.

KU KARANTA: Da duminsa: Bidiyon 'yan fashi da makami suna balle banki, sun kwashe makuden kudade

Dakarun soji sun tarwatsa sansanin 'yan bindiga a iyakar Kaduna da Niger
Dakarun soji sun tarwatsa sansanin 'yan bindiga a iyakar Kaduna da Niger. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Jigo a APC ya sanar da yadda zai haye shugabancin Legas duk da adawa

A cewarsa, wata rundunar sojin sama taje sintiri wuraren Kajari da Kugosi, inda suka hangi 'yan bindiga wurin Kawuri, iyakar Kaduna da jihar Neja.

Ya ce sojojin sun yi sa'ar ritsa 'yan bindigan inda suka same su har sun banka wa gidaje da wuraren bauta wuta.

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta tabbatar da yadda kwanan nan za ta kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

Kakakin rundunar soji, John Enenche, ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin taron bayar da bayani a kan ayyukan rundunar soji. A cewarsa, ta yadda sojoji suke ragargazar 'yan ta'adda, kwanan nan za su zama tarihi.

Ya kara da cewa: "Rundunar Operation Hadarin Daji da sauran rundunoni masu taimakonsu suna ragargazar 'yan ta'addan arewa maso yammacin kasar nan kuma suna samun nasarori na ban mamaki."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel