2023: Mulkin karba-karba ba zai shawo kan matsalolin Najeriya ba, El-Rufai

2023: Mulkin karba-karba ba zai shawo kan matsalolin Najeriya ba, El-Rufai

- Gwamna El-Rufai ya roki Najeriya da ta bar batun tsarin karba-karba wurin zaben Shugaban kasa

- Duk da dai A ranar Litinin, 23 na Nuwamba, Fashola ya bukaci a cigaba da yarjejeniyar karba-karba

- El-Rufai ya ce mulkin karba-karba ba zai gyara matsalolin da Najeriya take fuskanta ba

Akasin kiran da ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola yayi na batun karba-karba tsakanin yankunan Najeriya wurin mulki, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce karba-karba ba zai taimaki Najeriya ba, ko kuma kawo karshen matsalolin da kasar nan take fuskanta ba.

Premium Times ta ruwaito yadda gwamnan yayi wannan jawabin a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, yayin da yake jawabi a kan yadda 'yan Najeriya daga kowanne yanki suke kwadayin mulki, a taron NES.

El-Rufai ya ce batun karba-karba ba zai taimaki kasa ba.

Legit.ng ta tattara bayanai a kan yadda batun shugabanci karba-karba tsakanin arewa da kudu ya zama al'ada tun da aka fara siyasa a 1999.

El-Rufai ya ce cancanta ya kamata a yi amfani dashi wurin zaben shugaban kasar Najeriya.

KU KARANTA: Dalilin da yasa Ganduje ya ke son kawo sauyi a tsarin masarautun Kano

2023: Mulkin karba-karba ba zai shawo kan matsalolin Najeriya ba, El-Rufai
2023: Mulkin karba-karba ba zai shawo kan matsalolin Najeriya ba, El-Rufai. Hoto daga Nasir El-Rufai
Asali: UGC

KU KARANTA: Shugaban makaranta ta rasu bayan yanke jiki da ta yi ta fadi yayin jawabi (Bidiyo)

A wani labari na daban, wasu miyagu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai hari yankin Yolde pete da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.

Mazauna yankin tare da jami'an tsaro sun tabbatar da cewa, miyagun dauke da makamai sun tsinkayi gidan dansanda makusancin Atiku Abubakar.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, an gano cewa 'yan bindigan sun so tarar da dan sandan ne bayan sun zargi sun iso gari tare da Atiku Abubakar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel