Yan makarantan sakandare 80 sun ajiye karatu, sun ce sun gaji

Yan makarantan sakandare 80 sun ajiye karatu, sun ce sun gaji

- Saboda tsaurin malaminsu, daliban sakandare sun yi kaura daga makaranta

- Sun ce ba zasu koma ba sai lokacin jarabawa da zasu rijistan jarabawan karshe

- Shugaban makarantan ya yi kira ga iyaye su dawo da yaransu makaranta

Wasu yan aji karshe a makarantan sakandare sun fita daga makaranta a gabashin kasar Kenya ranar Laraba suna masu cewa gaskiya sun gaji da karatu.

A cewar jaridar Standard, wadanda yara yan makaranta Matungulu Boys Secondary School ne. Yanzu dalibai 36 kadai suka rage a makarantan.

Shugaban makarantan yace daliban na fuskantar ukubar laifukan da suka aikata ne shi yasa.

Wasu daga cikin daliban sun bayyanawa gidajen rediyo cewa shugaban makarantan ya nada tsauri kuma sun gaji da karatun.

Sun ce gwara su koma gida su zauna har sai lokacin zana jarabawan karkare sakandare yayi a shekarar 2021.

Shugaban makarantan ya bukaci iyayen yaran su dawo da su makaranta.

An bude makaranta a watan Oktoba domin daliban ajin karshe masu zana jarabawa su koma bayan an dan samu sauki annobar cutar Korona.

KU KARANTA: Yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna diban mutane, Sarkin Musulmi

Yan makarantan sakandare 80 sun ajiye karatu, sun ce sun gaji
Yan makarantan sakandare 80 sun ajiye karatu, sun ce sun gaji Hoto: @TheNationNews
Source: Twitter

KU DUBA: Yan bindiga sun budewa babban Sarkin Gargajiya wuta, sun kashe shi:

A wani labarin daban, Mai martaba sarkin Musulmi kuma Sultan na Sakkwato, Alhaji Abubakar Sa'ad III, ya yi tsokaci a kan matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki da Najeriya ke fama da su a yanzu haka.

Sultan, da yake jawabi a wajen taron majalisar shugabannin addinai ta kasa, ya bayyana cewa yadda albasa ta yi tsada ya tabbatar da girman wahalar tattalin arzikin da ake ciki a yanzu a Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel