Ba zamu yarda yan bindiga suna binmu gida sun sacemu ba, Zulum

Ba zamu yarda yan bindiga suna binmu gida sun sacemu ba, Zulum

- Zulum ya bukaci gwamnonin yankinsa su tashi tsaye kafin rikicin yan bindiga yayi kamari

- Gwamnan ya gana da gwamnonin Arewa maso gabashin Najeriya

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya zama wajibi Arewa ta tashi tsaye ta dauki matakin da ya dace kan yan bindigan da suka addabi mutane a gidajensu.

Zulum ya bayyana hakan ne a taron kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas karkashin jagoranicnsa.

Wannan shine karo na uku da zasu hadu su tattauna, rahoton BBC Hausa.

Zulum ya ce dubi ga yadda matsalar rashin tsaro ta tabarbare a Arewa maso yamma irinsu Kano da Kaduna, akwai bukatar su tashi tsaye kada hakan ya shigo yankinsu.

Ya ce wajibi gwamnonin tabbatar da amince ga matafiyan a titunan da suka hada jihohin.

KU DUBA: Dole a kare Jami’o’i da sauran wurare daga hare-haren ‘Yan bindiga inji Majalisa

Ba zamu yarda yan bindiga suna binmu gida sun sacemu ba, Zulum
Ba zamu yarda yan bindiga suna binmu gida sun sacemu ba, Zulum Hoto: Governor Borno
Source: Twitter

Bayan haka, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar II, ya yi Alla-wadai da lamarin tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya, inda yace yan bindiga na cin karansu ba babbaka.

Sarkin Musulmi wanda shine shugaban majalisar koli ta lamuran addini a Najeriya ya bayyana cewa yanzu yan bindiga gida-gida suke bi suna awon gaba da mutane a Arewa.

Alhaji Sa'ad ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, yayin taron majalisar hadin kan addinai NIREC da akayi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: Hukumar Soji ta karawa marigayi Kanal Bako girma zuwa Birgediya Janar don karramashi

A cikin 'yan kwanakin jami'ar ABU Zariya ta na fuskantar barazana bayan an sace wata malamar asibiti da kuma wani Farfesa a sashen koyar da aikin likitanci.

Bayan haka, masu garkuwa da mutane sun shiga makarantar Nuhu Bamalli, sun sace wani malami da yara biyu, an harbi wani Bawan Allah a dalilin harin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel