Gwamna El-Rufa'i yace ƴan Arewa masu son kai ne ke adawa da gyara da sauye sauye.

Gwamna El-Rufa'i yace ƴan Arewa masu son kai ne ke adawa da gyara da sauye sauye.

- Da alama muhawara a kan yi wa tsarin gudanar da gwamnatin Najeriya kwaskwarima da gyare-gyare ba zata kare ba

- A ranar Talata ne gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya halarci wani taro da aka yi a kan tattalin arziki wanda aka yi ranar Talata a Abuja

- Yayin taron, El-Rufa'i ya sake tabo batun tare da yin bayani a kan ma su sukar lamarin daga yankin arewa

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, kuma shugaban kwamitin gyara da sauye sauye a APC, ya yi tsokaci akan ƴan arewa masu adawa da gyara da sauye sauyen ƙasa, ya ce suna yin hakan ne bisa dalilinsu na son rai da zuciya, ba don cigaban al-umma ba.

A cewarsa, ƙudirin da kwamitinsa ya ƙirƙira akan sauye sauye a watan Junairu 2018 an jingineshi bisa tsoron shigar da siyasa cikinsa sakamakon tunkarowar zaɓen shekarar 2019.

Sai dai kalaman na El-Rufa'i sun jawo hankalin ƙungiyoyin zamantakewa da siyasa na ƙabilun Yoruba da takwararta Igbo, wato Afenifere ta Yoruba, da Ohanaeze Ndigbo ta Inyamurai.

KARANTA: Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas

Kungiyoyin, dukkansu daga kudancin Najeriya, sun bayyana kalaman El-Rufa'i a matsayin yaudara da wasa da hankalin ƴan kasa.

Amma gwamnan, wanda ya yi magana lokacin amsa tambayoyi yayin taron tattalin arziƙin Najeriya karo na 26 dake gudana a halin yanzu a Transcorp Hilton, Abuja, ya nuna cewa akwai mabanbantan matsaya daga ɓangaren Ƙungiyar Dattijan Arewa (NEF) dangane da gyara da sauyen sauyen da kuma sauran ƴan arewa a matsayin mutane.

Gwamna El-Rufa'i yace ƴan Arewa masu son kai ne ke adawa da gyara da sauye sauye.
Gwamna El-Rufa'i yace ƴan Arewa masu son kai ne ke adawa da gyara da sauye sauye.
Asali: UGC

Ya yi iƙirarin cewa akwai sama da mutane miliyan ɗaya ƴan arewa waɗanda suka amince da wannan tsarin, inda ya kafe akan cewa kowacce irin moriya da za'a samu daga gyaran ba iya yankin arewa da mutanenta bane zasu mora.

KARANTA: Buhari ya tsame rukunin wasu ma'aikata daga biyan haraji

"Ba wani muhimmanci da arewa keda shi a karkashin tsarin da Najeriya ke kai a halin yanzu, ba kuma wata moriya da Arewa ke ci.

"Mun fi kowa yawan yaran da basa zuwa makaranta. Mun fi kowa talauci. Mun fi kowa yawan faɗuwar jarrabawar JAMB. To, wace irin moriya ƴan arewa ke samu a wannan halin da muke ciki?

"A matsayina na gwamnan jihar Kaduna, na yi duba da matsalolin nan kuma na yi ƙoƙarin yadda mutanen jihata zasu hau tsani don cigaba. Ina tunanin kuna buƙatar tantancewa tsakanin kaɗan da kuma muryar waɗanda sukayi shiru masu rinjaye," a cewarsa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel