Bayan yiwa dokokin Shari'ar Musulunci kwaraskwarima, Dubai (UAE) ta haramtawa yan kasashen Musulmai 13 shiga kasar

Bayan yiwa dokokin Shari'ar Musulunci kwaraskwarima, Dubai (UAE) ta haramtawa yan kasashen Musulmai 13 shiga kasar

Hadaddiyar daular Larabawa UAE wacce aka fi sani da Dubai ta daina bada biza ga yan wasu kasashe 13, yawanci na Musulmai daga yanzu, cewar wani takarda a wata cibiyar shakatawa ta saki.

An aika wannan takarda da Reurters ta gani ga dukkan kamfanonin da wajen shakatawan, kuma an fara dabbaka dokar tun ranar 18 ga Nuwamba.

Kasar UAE bata bayyana dalilin da yasa aka kafa wannan doka ba.

Ga jerin kasashen:

1. Iran

2. Turkey

3. Syria

4. Somalia

5. Afghanistan

6. Libya

7. Algeria

8. Kenya

9. Iraq

10. Lebanon

11. Pakistan

12. Tunisiya

13. Kenya

Hukumomin kasar ba tayi tsokaci kan lamarin ba har yanzu.

KU KARANTA: Baka isa ka tafi da kujeranmu ba - Uwar jam'iyyar PDP ta gargadi Sanatan da ya sauya sheka APC

Bayan soke amfani da Shari'ar Musulunci, Dubai (UAE) ta haramtawa yan kasashen Musulmai 13 siga kasar
Bayan soke amfani da Shari'ar Musulunci, Dubai (UAE) ta haramtawa yan kasashen Musulmai 13 siga kasar Hoto: Burj
Asali: UGC

KU KARANTA: Zan kwace mulki hannun Gwamna Fintiri a 2023, Sanata Ishaku Abbo

A kokarinta na bunkasa tattalin arzikin kasarta da zamantakewa, hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi wa wasu dokokin shari’ar Musuluncin kasar gyaran fuska, inda a yanzu ta halasta shan giya da zaman dadiro.

Wannan kwaskwarima da kasar ta yi yana zuwa ne a daidai lokacin da ta ke ci gaba da daukar hankulan masu zuwa yawon bude ido musamman daga kasashen Yamma.

A ganin UAE hakan da ta yi zai habbaka tattalin arzikinta tare da nuna wa duniya cewa ita kasa ce mai sassaucin ra’ayi, karbar sauyi da kuma tafiya da zamani.

Wannan yunkuri ya biyo bayan wata yarjejeniya mai cike da tarihi da kasar ta dauka domin dawo da hulda tsakanin UAE da kasar Isra’ila, wacce ita ma ake sa ran za ta kara yawan masu yawon bude ido da zuba hannun jari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel