Shugaban makaranta ta rasu bayan yanke jiki da ta yi ta fadi yayin jawabi (Bidiyo)

Shugaban makaranta ta rasu bayan yanke jiki da ta yi ta fadi yayin jawabi (Bidiyo)

- Hakika dukkan mai rai mamaci ne, sannan a duk lokacin da mutuwa ta so daukar mutum tana iya zuwa

- Hajiya Bisola Rahama Zakariyya tana sanye da hijabi da takunkumin fuska, tana tsaka da jawabi aka ga ta fadi

- Shugabar makarantar Elkanemi ta amsa kiran mahaliccin ta a ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba, tana cikin jawabi

Hajiya Bisola Rahama Zakariyya, shugabar Ekkanemi College of Islamic Theology da ke Maiduguri, ta rasu tana tsaka da gabatar da jawabi, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Al'amarin ya faru ne a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba. Matar tana sanye da hijabi da takunkumin fuska, tana tsaka da gabatar da jawabi sai ta rasa inda kanta yake, take a nan baki masu saurin tunani suka yi gaggawar zuwa gareta.

Kamar yadda bayanai suka kammala, an yi gaggawar kai ta ICU, duk da ba a sanar da na wanne asibiti bane. Sai dai ta amsa kiran mahaliccinta a ranar 23 ga watan Nuwamba.

Shugaban makaranta ta rasu bayan yanke jiki da ta yi ta fadi yayin jawabi (Bidiyo)
Shugaban makaranta ta rasu bayan yanke jiki da ta yi ta fadi yayin jawabi (Bidiyo). Hoto daga metrowatchonline.com
Asali: Facebook

KU KARANTA: Elon Musk ta ture Bill Gates, ya zama mutum mafi arziki na 2 a fadin duniya

Sardaunan Alanjirori, malami a jami'ar jihar Yobe, yayi amfani da shafinsa na Twitter da daddaren Litinin, inda ya nuna alhininsa game da rasa matar, wacce yace ba asara ce ga 'yan Elkanemi kadai ba, har ga jihar Borno da Najeriya gabadaya.

Kamar yadda ya wallafa: "Hakika dukkan mai rai mamaci ne! Ina mika sakon ta'aziyya ta ga daliban makarantar Elkanemi da ke Maiduguri, bisa mutuwar fuji'ar da shugabar makarantar, bangaren mata tayi. Wannan babbar asara ce ga 'yan Elkanemi, jihar Borno da Najeriya gabadaya."

KU KARANTA: Mata ta tana lalata da fastonmu da kuma dattawan cocinmu, Magidanci

A wani labari na daban, rundunar Operation Thunder Strike ta mayar da harin 'yan bindiga da daren Litinin a hanyar Kaduna zuwa Abuja. An gano yadda 'yan ta'adda suka tsere cikin daji da raunika saboda sojojin sun hana su cin karensu babu babbaka.

Kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan yace, 'yan bindigan sun kafa daba wuraren Kakau da shirin harbi, sojoji suka kai musu hari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel