Sojin Najeriya sun fatattaki 'yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun ragargaza wasu

Sojin Najeriya sun fatattaki 'yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun ragargaza wasu

- Rundunar OPTS tana samun nasarar ragargazar 'yan bindiga a jihar Kaduna

- Rundunar ta mayar da harin 'yan bindiga a titin Kaduna zuwa Abuja

- Sojojin sun kuma ragargaji 'yan bindiga a titin Zaria zuwa Funtua

Rundunar Operation Thunder Strike ta mayar da harin 'yan bindiga da daren Litinin a hanyar Kaduna zuwa Abuja. An gano yadda 'yan ta'adda suka tsere cikin daji da raunika saboda sojojin sun hana su cin karensu babu babbaka.

Kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan yace, 'yan bindigan sun kafa daba wuraren Kakau da shirin harbi, sojoji suka kai musu hari.

"Da rundunar suka gyara cunkoson titin, sai su a gano cewa 'yan bindiga sun bugi wani direba. Sannan wasu motoci 2 sun fada daji, saboda tsoron 'yan bindigan, wanda hakan yayi sanadiyyar jin ciwon wasu fasinjoji da ke cikin mota, jami'an tsaro sun yi gaggawar wucewa da su asibiti.

Sojin Najeriya sun fatattaki 'yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun ragargaza wasu
Sojin Najeriya sun fatattaki 'yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun ragargaza wasu. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: ASUU: 'Ya'yana 3 ne suke jami'o'in gwamnatin Najeriya, Ngige

"Sannan an sanar da gwamnati yadda jami'an tsaro suka ragargaji 'yan bindiga a titin Zaria zuwa Funtua, a karamar hukumar Giwa da safiyar Talata.

"Sun samu nasarar ceto mutane 2 sannan aka yi gaggawar kai su asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Shika. Duk da haka jami'an tsaron suna cigaba da sintiri a wuraren.

"Gwamnatin jihar ta tura sakon ta'aziyyar wadanda suka rasa rayukansu, da fatan za su samu rahamar Ubangiji, sannan yana fatan marasa lafiya su samu lafiya da gaggawa," kamar yadda takardar tazo.

KU KARANTA: A cikin sa'o'i 6, budurwa ta tashi daga Legas zuwa Benin kuma ta koma Legas a babur

A wani labari na daban, rundunar Operation Fire Ball ta arewa maso gabas ta ragargaji 'yan bindiga 23, sannan ta kwashe wani abu mai fashewa a hannunsu, wuraren Ngamdu, kusa da Maiduguri.

Mukaddashin jami'in hulda da jama'a, Birgediya janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan a ranar Talata, inda yace wasu daga cikin 'yan bindigan sun sha ragargaza yayin kokarin amsar kudaden fansa daga hannun iyalan wadanda aka yi garkuwa dasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: