Elon Musk ta ture Bill Gates, ya zama mutum mafi arziki na 2 a fadin duniya

Elon Musk ta ture Bill Gates, ya zama mutum mafi arziki na 2 a fadin duniya

- A shekarar 2020, Elon Musk ya maye gurbin Bill Gates, wanda yanzu haka, shine mutum na 2 a kudi, duk duniya

- Elon Musk, CEO din Tesla ne, yana da dukiya mai kimar dala biliyan 127.9, daidai da N48,755,480,000,000

- Tun 2017, Jeff Bezos ya doke Bill Gates, inda ya zama mai kudin kaf duniya, kuma har yau shi din ne

CEO din Tesla, Elon Musk, yanzu haka ya maye gurbin Bill Gates, don yanzu haka shine mutum na 2 a kudi kaf duniya.

Duk da annobar coronavirus ta shekarar 2020 wacce ta girgiza tattalin arzikin duniya, amma dukiyarsa habaka tayi.

A cewar Bloomberg, yanzu haka Musk yana da dukiya mai kimar dala biliyan 127.9, wanda yayi daidai da N48,755,480,000,000.

Elon Musk ta ture Bill Gates, ya zama mutum mafi arziki na 2 a fadin duniya
Elon Musk ta ture Bill Gates, ya zama mutum mafi arziki na 2 a fadin duniya. Hoto daga Wierd, USnews.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: CCB za ta gurfanar da Magu a kan wata kadara da wani asusun banki

Legit.ng ta lura da yadda biloniyan ya hada dala biliyan 100.3, daidai da N38,234,360,000,000 na dukiyarsa ta 2020.

Elon Musk ya riga ya maye matsayin Bill Gates, don yanzu haka shine mutum na 2 a kudi, duk duniya.

Bill Gates, wanda shine CEO din Microsoft Corporation, yana da dukiya mai kimar dala biliyan 127.7, daidai da N48,679,240,000,000. Kudin da yakamata ya nunka hakan da a ce ba ya bayar da sadaka cikin shekarun da suka gabata zuwa yanzu ba.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi barazanar lalata da diyarmu idan bamu kai kudi ba, Iyayen budurwa

Jeff Bezos ne ya maye gurbinsa a 2017, inda ya zama wanda yafi kowa dukiya a duniya, kuma har yanzu yana nan a matsayinsa. Gates ya bayar da kyautar fiye da dala biliyan 27 ta hanyar gidauniyarsa tun daga 2006 zuwa yanzu.

A wani labari na daban, wata 'yar Najeriya, mai suna Igwe Munachimso, ta ce ya kamata 'yan yankin kudu maso gabas su rage sadakinsu, tun bayan dan uwanta ya auri wata 'yar Benue da sadaki kasa da N50,000.

Munachimso ta bayyana wannan shawararta a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ta bayyana abubuwan da aka bukaci yayanta ya kai na al'adar Benue.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel