A taimaka a rage dukiyar aure ko 'yan mata za su samu shiga, budurwa ta roki iyaye

A taimaka a rage dukiyar aure ko 'yan mata za su samu shiga, budurwa ta roki iyaye

- Wata budurwa mai suna Igwe Munachimso ta bukaci 'yan kabilar ibo da su rage kudin sadaki

- Budurwar ta ce yayanta ya auri wata 'yar jihar Benue, kuma kudin da ya kashe bai wuce N50,000 ba

- Ta bayar da wannan shawarar ne a shafinta na Twitter, inda tace ya kamata a duba kuma a gyara

Wata 'yar Najeriya, mai suna Igwe Munachimso, ta ce ya kamata 'yan yankin kudu maso gabas su rage sadakinsu, tun bayan dan uwanta ya auri wata 'yar Benue da sadaki kasa da N50,000.

Munachimso ta bayyana wannan shawararta a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ta bayyana abubuwan da aka bukaci yayanta ya kai na al'adar Benue.

Kamar yadda ta wallafa: "A gaskiya 'yan kabilar ibo ne ke tsanantawa a harkar aure. Gaba daya abinda yayana ya kashe wurin auren matarsa a Otuko, jihar Benue bai wuce N50,000 ba. Yakamata mu gyara, mu kuma rage tsanantawa a aure."

Budurwa ta roki iyaye Ibo da su sassauta dukiyar aure ko mata za su samu mazan aure
Budurwa ta roki iyaye Ibo da su sassauta dukiyar aure ko mata za su samu mazan aure. Hoto daga @SpecimenIgwe
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakarun soji sun dakile bai wa 'yan Boko Haram kudin fansa, sun ragargaza mayakan

Bayan ta yi wannan wallafar ne mutane suka yi ta tsokaci a kai.

Wani Eduagbo ya ce: "Ki tambayar min yayanki idan matarsa tana da kanwa, Ki taimakamin."

Wani talk2middle cewa yayi: "Ki kyale mu mana. Za ki iya zuwa kiyi aure acan."

Wata Nemzolee ta ce "wanda ba shi da kudi yaje yayi aurensa a Benue."

Da sauran tsokaci iri-iri da mutane suka yi ta yi. Wasu suna yaba mata, wasu kuma suna caccakarta.

KU KARANTA: An kama matasa biyu dauke da akwatin gawa dankare da rigunan nono da dan kamfai na mata

A wani labari na daban, wata jarumar fina-finan Nollywood, Didi Ekanem, ta ce kwanan nan wasu 'yan sanda a jihar Legas suka ci mata zarafi. Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da labarin ranar Lahadi, kusan 'yan sanda 10 ne suka ci mata zarafi saboda ta saba dokar titi.

A cewarta, al'amarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Nuwamba, wuraren Lekki a jihar Legas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel