ASUU: 'Ya'yana 3 ne suke jami'o'in gwamnatin Najeriya, Ngige

ASUU: 'Ya'yana 3 ne suke jami'o'in gwamnatin Najeriya, Ngige

- Chris Ngige, ministan kwadago da ayyuka, ya ce yana da yara 3 a jami'o'in gwamnati

- Ministan ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a kan yajin aikin ASUU

- Ya ce ASUU bata isa tace bai damu ba, don ya tsaya tsayin-daka a kan lamarin

Ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, yace yana da yara 3 a jami'o'in gwamnati da ke kasarnan, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Ministan ya fadi hakan a wata tattaunawa da Arise TV suka yi dashi a kan yajin aikin malaman jami'a, wanda ya dakatar da karatun yara da dama.

Ngige ya ce yana daya daga cikin iyayen daliban jami'o'in gwamnatin Najeriya, yana zargin 'yan kungiyar ASUU da tura yaransu jami'o'in kudi.

ASUU: 'Ya'yana 3 ne suke jami'o'in gwamnatin Najeriya, Ngige
ASUU: 'Ya'yana 3 ne suke jami'o'in gwamnatin Najeriya, Ngige. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda rashawar N100,000 ta jefa dan sanda mai mukamin DSP babbar matsala

A cewarsa, "Ina da yara 3 a makarantun gwamnati. A makarantun gwamnati suke; ba jami'o'i masu zaman kansu ba. Ba kamar 'yan kungiyar ASUU ba duk sun tura yaransu jami'o'in kudi, ni kuwa ina da 3 anan. Don haka ina da ruwa da tsaki a makarantun gwamnati.

"Don haka idan ASUU ta ce 'yan siyasa basu damu da lamarin ba saboda sun tura yaransu kasashen waje, Chris Ngige ya damu, saboda yaransa suna karatu a nan kasar, duk da 2 daga cikinsu suna da shaidar zama Amurka amma na zabi su zauna nan tare da ni.

"Don haka, ASUU ba su isa su zargeni da rashin kishin kasa ba. Ina yin iyakar kokarin ganin na taimaki jami'o'in kasar nan."

KU KARANTA: Da duminsa: CCB za ta gurfanar da Magu a kan wata kadara da wani asusun banki

A wani labari na daban, a ranar Juma'a, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce yankin arewa ta tsakiya za su ciyar da kasar nan gaba. A cewar Saraki, yankin ne zai kawo mafita ga Najeriya nan gaba, The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda yace, arewa ta tsakiyar tana da ma'adanai masu tarin yawa, wanda hakan zai kawo kudi Najeriya. Saraki ya bayyana hakan ne bayan shugabannin kungiyar jama'an arewa ta tsakiya (NCPF) sun kai masa ziyara gidansa da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng