Da duminsa: Sojin Najeriya sun bankado wani harin 'yan bindiga a Kaduna

Da duminsa: Sojin Najeriya sun bankado wani harin 'yan bindiga a Kaduna

- Sojojin Najeriya sun samu nasarar mayar da harin 'yan ta'adda a karamar hukumar Igabi

- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan

- Aruwan ya tattauna da shugabannin unguwannin, inda ya shawarcesu da su hada kai da jami'an tsaro

Sojojin Najeriya sun dakatar da harin wasu 'yan bindiga a anguwar Sabon Birni da ke karamar hukumar Igabi a cikin jihar a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba.

Gidan talabijin din Channels, sun ruwaito yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan.

Kwamishinan ya yaba wa rundunar a kan yadda ta mayar da harin da aka kai. Kamar yadda jaridar Channels ta ruwaito, fiye da mutane 11 ne suka rasa rayukansu a karamar hukumar.

Da duminsa: Sojin Najeriya sun bankado wani harin 'yan bindiga a Kaduna
Da duminsa: Sojin Najeriya sun bankado wani harin 'yan bindiga a Kaduna. Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

KU KARANTA: An kama matasa biyu dauke da akwatin gawa dankare da rigunan nono da dan kamfai na mata

A wannan harin kuwa, sojoji sun shirya musu, inda wasunsu suka tsere da raunuka. Duk da dai har yanzu mazauna wurin suna cikin matsanancin tashin hankali da fargaba, har suna neman a kara yawan jami'an tsaro a anguwar.

Kwamishinan ya gana da shugabannin anguwar, inda ya rokesu da su hada kawunansu don jami'an tsaro su samu su yi ayyukansu yadda ya dace.

KU KARANTA: Dan sanda ya yi kokarin lalata da ni har da yunkurin latsa min nono - Jaruma Didi

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya suna cigaba da samun nasarar ragargazar 'yan Boko Haram a kauyakun waje-wajen babban birnin Borno, Maiduguri.

Mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar soji, birgediya janar Benard Onyeuko, yace runduna ta 251 ta bataliyar soji ta kaiwa wasu 'yan Boko Haram farmaki a Molai.

A cewarsa, sai da sojojin suka yi nazari kwarai, kuma suka yi amfani da dabara ta musamman, bayan iyalan wasu mutane da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su sun bukaci Naira Miliyan 2 a hannunsu sun kai musu rahoto.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel