'Yan bindiga sun yi barazanar lalata da diyarmu idan bamu kai kudi ba, Iyayen budurwa
- Iyayen daliban ABU da aka sace a hanyarsu ta zuwa Badagry sun koka a kan tashin hankalin da suka shiga
- Daya daga cikin iyayen ya ce, ya bayar da fiye da N500,000 don masu garkuwa da mutane su saki diyarsa amma sun ki
- Sun tsoratar da iyayen yara matan da cewa indai ba su biya su kudin ba, za su auresu ko kuma su yi ta lalata dasu
Daya daga cikin iyayen daliban jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, jihar Kaduna da masu garkuwa da mutane suka sace a makon da ya gabata, ya ce wadanda suka yi garkuwa da diyarsa sun ce za su yi ta lalata da ita matsawar bai yi gaggawar kai kudaden da suka bukata a wurinsa ba.
Daliban, 'yan fannin yaren faransa ne, wadanda suka kama hanyar zuwa NFLV da ke Badagry ne lokacin da aka yi garkuwa da su.
Ashiru Zango, shugaban jami'an tsaron ABU, ya shaida wa TheCable cewa an sake su, amma bai fadi yadda aka yi aka sakesu ba.
A wata hira da TheCable tayi da mahaifin daya daga cikin daliban da aka sace, ya ce ya biya fiye da N500,000 yana rokon masu garkuwa da mutanen da su sakar masa diyarsa.
A cewarsa, "Sun kirani jiya (Asabar), inda suka ce indai har ban biya Naira miliyan 1 ba, za su kashe yara matan ko su auresu, ko kuma su dinga lalata da su."
Duk da mahaifin ya bukaci kada a ambaci sunansa, ya ce sun yi zaton jami'an tsaro za su taimaka musu fiye da haka.
KU KARANTA: Dakarun soji sun dakile bai wa 'yan Boko Haram kudin fansa, sun ragargaza mayakan
"Bayan mun iso Kaduna, an shaida mana cewa jami'an tsaro sun shiga daji neman masu garkuwa da mutane. Amma sai ga 'yan ta'addan sun kiramu, cewa mu tsaya daidai junction din Abuja," a cewarsa.
"Sun tura mana lambar wayar da za mu kira. Da muka kira, mutumin ya zo ya daukemu cikin mota. Ashe shima an sace masa diyarsa ne.
"Mun isa wuraren titin Kaduna zuwa Abuja, wuraren karfe 11 na dare don mu kai kudade da abubuwan da suka bukata," ya kara da cewa.
KU KARANTA: An kama matasa biyu dauke da akwatin gawa dankare da rigunan nono da dan kamfai na mata
Dickson Oko, daya daga cikin daliban da ya samu nasarar tserewa, duk da dai an harbeshi, yace masu garkuwa da mutanen sun bukaci naira miliyan 30 wurin iyayen yaran, don a sakesu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng