Sabuwar cuta ta barke a Filato sakamakon cin wawason tallafin korona

Sabuwar cuta ta barke a Filato sakamakon cin wawason tallafin korona

- Fiye da mutane 20 sun fadi ciwo a wani kauye da ke jihar Filato

- Bayan jama'an sun sha wani kunu duk suka barke da zawo

- Kuma alamu sun nuna cewa geron da aka yi kunun ne mai matsalar

Fiye da mutane 20 sun fadi ciwo a kauyen Joi dake jihar Filato, bayan sun sha wani Kunu da akayi da gero, kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar wa da Premium Times.

Kauyen yana cikin karamar hukumar Riyom da ke jihar Filato. Wadanda cutar ta kama sun hada da dagacin kauyen mai suna Stephen Jugu, wanda ya samu lafiya cikin ranakun karshen mako.

Kamar yadda bayanai suka kammala, an siyo geron ne a hannun wani mai karamin shago a kasuwar anguwar, ranar Talata.

Sabuwar cuta ta barke a Filato sakamakon cin wawason tallafin korona
Sabuwar cuta ta barke a Filato sakamakon cin wawason tallafin korona. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: An kama matasa biyu dauke da akwatin gawa dankare da rigunan nono da dan kamfai na mata

Kamar yadda Jugu, wanda sakataren wata coci ne, ya tabbatar da yadda fiye da mutane 20 suka shiga cikin matsanancin hali bayan sun sha kunun a ranar Litinin.

"Na farka da tsakar dare ina ta zawo, hakan ya cigaba har safiya. Sai na gano ashe saboda wannan kunun da na sha ne. Sai daga baya na gano duk wadanda muka sha kunu tare sun fuskanci irin hakan. Kusan mutane 20 ne, amma yanzu duk an sallamesu daga asibiti," yace.

Shugaban anguwar, wanda ya tabbatar da duk wadannan mutanen sun fadi ciwon, ya ce sun sanar da shugaban bunkasa anguwanni yadda lamarin ya auku.

KU KARANTA: Dan sanda ya yi kokarin lalata da ni har da yunkurin latsa min nono - Jaruma Didi

"Sun je sun siyo gero wurin wani mutum mai karamin shago. Sai wata mata ta hada kunu dashi, ta rabawa 'yan uwa da abokan arziki. Duk wadanda suka sha kunun sun barke da zawo. Wasu daga cikinsu har suma suka yi ta yi, wasu suna kashin jini.

"Duk sai da su ka kwanta asibiti, inda aka basu magani," kamar yadda Tim Danchal, shugaban kungiyar habaka anguwar Jol, ya tabbatar.

Danchal ya ce, har yanzu hukuma tana cigaba da bincike a kan lamarin.

A wani labari na daban, CCB za ta gabatar da Magu, tsohon shugaban EFCC gaban CCT, daga yanzu zuwa kowanne lokaci, kamar yadda TheCable ta fahimta.

Kamar yadda labarai suka bayyana, za a yanke wa Magu hukunci saboda kin ambaton wani asusun bankinsa yayin cike takardar bayyana kadarori.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel