NLC: Abin da ya fusata mu har muka fice daga tattaunawa da FG a kan karin farashin fetur

NLC: Abin da ya fusata mu har muka fice daga tattaunawa da FG a kan karin farashin fetur

- Taron da aka shirya a daren ranar Lahadi a tsakanin FG da NLC a fadar shugaban kasa bai samu yiwuwa ba

- A cikin watan Satumba ne NLC ta yi niyyar shiga yajin aiki biyo bayan karin farashin man fetur da na wutar lantarki

- Sai dai, NLC ta jingine batun shiga yajin aikin bayan samun fahimtar juna da kuma kulla yarjejeniya da FG

Hadaddiyar kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta zargi gwamnatin tarayya (FG) da nuna rashin gaskiya yayin tattaunawarsu domin nemo mafita a kan karin farashin man fetur da na wutar lantarki.

NLC ta zargi FG da sabawa yarjejeniyar da suka cimma a tsakaninsu har ta kai ga an fasa shiga yajin aikin da aka yi niyyar farawa a cikin watan Satumba.

Kungiyar ta bayyana cewa hakan shine dalilin da yasa har mambobinta suka fusata, suka fice yayin ganawarsu da wakilan FG a daren ranar Lahadi.

KARANTA: 2023: Ba zamu taba lamunta a dauki Kirista daga arewa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa ba, Farfesa Mahuta

Kazalika, kungiyar ta bayyana cewa ba zata kara halartar wani zama da wakilan FG ba matukar ba'a fara janye karin farashin man fetur ba.

NLC: Abinda ya fusata mu har muka fice daga tattaunawa da FG a kan karin farashin fetur
NLC: Abinda ya fusata mu har muka fice daga tattaunawa da FG a kan karin farashin fetur @Vanguard
Asali: Twitter

A daren ranar Lahadi ne wakilan kungiyar NLC suka fusata tare da ficewa daga dakin taro na 'Old Banquet Hall' da ke fadar shugaban kasa jimmkadan bayan fara ganawarsu da wakilan FG domin tattauna sabon karin farashin man fetur.

KARANTA: Karin albashin Malamai: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin aiwatarwa

Yayin taron FG ta samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ministan kwadago da samar da ayyuka; Sanata Chris Ngige, da karamin minsitan kwadago, Festus Keyamo (SAN).

Sauran wakilan na FG sun hada da karamin ministan wutar lantarki, Yarima Godwin Jedy-Agba, da kuma karamin ministan albarkatun man fetur, Cif Timipre Sylva.

Da yake magana da manema labari ranar Litinin, mataimakin shugaban kungiyar NLC, Kwamred Joe Ajaero, ya bayyana cewa, "tun farko mun jingine batun shiga yajin aiki ne saboda fahimtar juna da muka samu da kuma yarjejeniyar da muka kulla.

"Gwamnati ta saba dukkan alkawura da yarjejeniyar da muka kulla kafin mu amince da jingine yajin aiki a ciki watan Satumba, mun fice daga wurin taron ranar bayan mun tuna musu sharudan da suka saba yayin taronmu na baya."

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na cewa ya matukar girgiza da samun labarin cewa tattalin arzikin Nigeria ya sake karyewa.

Wannan shine karo na uku da tattalin arzikin Najeriya ya sake karyewa a karkashin mulkin shugaba Buhari.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel