Bayan Dangote, FG ta sake wani hamshakin dan kasuwa a arewa daga dokar rufe iyakokin kasa

Bayan Dangote, FG ta sake wani hamshakin dan kasuwa a arewa daga dokar rufe iyakokin kasa

- Tun a cikin shekarar 2019 gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta na kan tudu; ba shiga, ba fita

- A cewar gwamnati, ta yi hakan ne domin bunkasa harkokin kasuwanci a cikin gida

- Tun bayan lokacin, babu labarin shige da fice da mafi yawan kayayyakin kasuwanci idan ba ta barauniyar hanya ba

Kamfanin siminti na BUA, mallakar hamshakin dan kasuwa, Abdulsamad Isiyaka Rabiu, ya samu sahalewar gwamnatin tarayya domin fitar da siminti zuwa ketare ta iyakar kan tudu, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin siminti na Dangote ya sanar da cewa ya samu izinin fitar da simiti ta kan iyakokin kan tudu zuwa kasar Nijar da Togo.

Wata takarda wadda Victor Dimka,Kwanturolan kwastam sashen tilasta doka da aiki ya sawa hannu don turawa mataimakin kwanturola na ƙasa,wadda gidan jaridar TheCable yayi tozali da ita tayi nuni da cewa sahalewar tazo ne daga ofishin mai bada shawarwari kan al'amurran tsaro na ƙasa.

KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun kashe jami'ai biyu, sun yashe ma'adanar makamai

"An umarce ni da turo wannan wasiƙar mai lamba NSA/227/C 17 ga watan Yuni 2020 daga ofishin mai bada shawarwari kan harkokin tsaro na ƙasa"a rubutun takardar.

"Motocin zasu fita kuma su dawo ta jan iyakar madakatar Illela a jihar Sakkwato.

"Kusa idanu don tabbatar da cewa motar ta ɗauki iya siminti zuwa jamhuriyyar Nijar sannan ta dawo Najeriya ba tare da komai ɗauke cikinta ba."

Bayan Dangote, FG ta sake wani hamshakin dan kasuwa a arewa daga dokar rufe iyakokin kasa
Abdulsamad Isiyaka Rabiu mai kamfanin BUA
Asali: Twitter

A watan Oktoba shekarar 2019, Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya bada umarnin rufe kan iyakokin ƙasar domin kawo karshen safarar makamai,kayan abinci,da muggan ƙwayoyi zuwa cikin ƙasar.

KARANTA: Ba haka bane Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

Rufe kan iyakokin wadda maƙasudinta shine bunƙasa noma da harkokin kasuwanci gami da ƙarfafa tsaro, ta taka muhimmiyar rawa wajen rushewar harkokin kasuwanci a ƙasashe irinsu Togo, Ghana, da Kwaddebuwa waɗanda suka dogara da Najeriya domin kasuwancinsu,al-ummomi sama da miliyan 200 ke ƙarƙashin waɗannan ƙasashe.

Kasuwanci da dama sun samu naƙasu sakamakon rashin samun damar fitar da kayayyakin da suke sarrafawa sanadiyyar rufe kan iyakokin.

Bayan Joe Biden ya zamanto zakaran da ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka,wani rahoto da jaridar Quartz Africa ta wallafa, ya yi hasashen yadda gwamnatin Biden zata canja alaƙar Amurka da Nahiyar Afirka bakiɗaya.

Legit.ng Hausa ta kalato muku wasu daga cikin abubuwan da rahoton ya ƙunsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel