Yadda rashawar N100,000 ta jefa dan sanda mai mukamin DSP babbar matsala
- An kama wani DSP da yaransa bisa laifin amsar cin hancin N100,000 a jihar Legas a hannun wata budurwa
- 'Yan sandan sun kama wata Ekanem, mai mota kirar Toyota Venza, mai lamba APP 775 GJ saboda rashin bin dokar titi
- Bayan an kammala bincike ne aka gano DSP din da yaransa suna da laifi dumu-dumu ne aka damko su
An kama wani DSP na 'yan sanda, wanda yake aiki a wuraren Lekki Ajah da ke jihar Legas, tare da yaransa a kan amsar cin hancin N100,000, jaridar Vanguard ta wallafa haka.
Shugaban bangaren laifuka na musamman akan harkokin jama'a, Adebayo Taofiq, ya fadi hakan a wata takarda ta ranar Lahadi, wacce ya gabatar wa da manema labarai na jihar Legas.
A cewar Taofiq, wata Didi Ekanem, mai mota kirar Toyota Venza, mai lamba APP 775 GJ, ce ta biya cin hancin. Bayan 'yan sandan sun kama ta da laifin rashin bin dokar titi wuraren babban titin Lekki Ajah.
KU KARANTA: Hukuncin Ubangiji na bi, na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, Umahi
A cewarsa, wajibi ne sakin labarin don yin martani ga labarin da jaridar Punch ta saki ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamban 2020 a feji na 31, mai taken "Kwamandan 'yan sanda ya nemi yin lalata da ni- Didi Ekanem".
"Shugaban rundunar ne ba kwamanda ba, kamar yadda suka ruwaito ta tura masa N100,000 ta asusun bankinsa.
"Sai da ta tura kudin, tukunna aka sakar ma ta motarta," cewar Taofiq.
Bayan shugaban rundunar, CSP Olayinka Egbeyemi ya gama bincike a kan al'amarin, ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, ya sa an kama DSP din, da yaransa.
KU KARANTA: Daga zuwa yin itace aka sace ta, sai dawowa gida ta yi da cikin dan Boko Haram
"Za a turasu babban ofishin 'yan sanda na jihar Legas, don a dauki mataki akansu," cewar shugaban bangaren.
Taofiq ya ce Egbeyemi ya ja kunnen masu ababen hawa, musamman masu motoci ko babura, da su dinga bin dokoki yadda ya kamata.
A cewarsa, duk wanda aka kama da irin wannan laifin zai fuskanci hukuncin kotu.
Ya kuma ja kunnen jama'a da su guji bai wa 'yan sanda cin hanci, don daga mai bayarwa, har mai amsa yana da laifi.
A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya suna cigaba da samun nasarar ragargazar 'yan Boko Haram a kauyakun waje-wajen babban birnin Borno, Maiduguri.
Mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar soji, birgediya janar Benard Onyeuko, yace runduna ta 251 ta bataliyar soji ta kaiwa wasu 'yan Boko Haram farmaki a Molai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng