Da duminsa: CCB za ta gurfanar da Magu a kan wata kadara da wani asusun banki

Da duminsa: CCB za ta gurfanar da Magu a kan wata kadara da wani asusun banki

- An gano cewa daga yanzu zuwa kowanne lokaci, CCB za ta iya gabatar da Magu gaban CCT

- Magu tsohon shugaban hukumar EFCC ne, wanda aka dakatar da shi saboda zargin rashawa

- An zarge shi da kin bayyana wasu dukiyoyin da ya mallaka a lokacin da za a daura shi a mukamin

CCB za ta gabatar da Magu, tsohon shugaban EFCC gaban CCT, daga yanzu zuwa kowanne lokaci, kamar yadda TheCable ta fahimta.

Kamar yadda labarai suka bayyana, za a yanke wa Magu hukunci saboda kin ambaton wani asusun bankinsa yayin cike takardar bayyana kadarori.

The Cable ta fahimci yadda wani asusun bankin Magu yake ajiye na tsawon shekaru 5, sannan CCB ta lissafo wasu wurare da ke Port Harcourt, jihar Rivers, wadanda mallakin kwamishinan 'yan sanda ne, amma aka yi amfani da su duk don a ci galaba wurin kayar da Magu.

Da duminsa: CCB za ta gurfanar da Magu a kan wata kadara da wani asusun banki
Da duminsa: CCB za ta gurfanar da Magu a kan wata kadara da wani asusun banki. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Daga zuwa yin itace aka sace ta, sai dawowa gida ta yi da cikin dan Boko Haram

An zargesa da mallakar dukiyoyi a Dubai, Legas da Abuja, amma yanzu duk ta bayyana cewa ba gaskiya bane duk wadannan zargin.

Lauyoyinsa sun ce gidansa daya ne, wanda yake Karu, jihar Nasarawa.

Wani lauyansa ya shaida wa TheCable cewa batun mallakar gida a Dubai da kuma Banana Island, jihar Legas da ake zargin Magu dashi, duk ba gaskiya bane.

Magu, wanda ya rike kujerar shugaban EFCC a shekarar 2015, da aka dakatar a watan Yulin 2020, CCB ta gayyace shi don ya amsa tambayoyi a kan dukiyoyin da ya mallaka.

KU KARANTA: Dakarun soji sun dakile bai wa 'yan Boko Haram kudin fansa, sun ragargaza mayakan

Wannan karon, Alkali Ayo Salami, ya binciki Magu, wanda hakan yayi sanadiyyar dakatar dashi da kuma yanke masa hukunci a kan rashawa a ofishinsa, laifin da kullum Magu yake musawa.

Magu ya ki bayyana gaban CCB, ganin an hana shi damar duba takardun da ya bukata.

A wata takarda ta ranar Lahadi, lauyan Magu, Wahab Shitu, ya musanta rashin zuwa kotun wanda yake karewa.

A wani labari na daban, a ranar Talata, Umahi ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, bayan 'yan satittuka da aka yi ta rade-radin fitarsa daga jam'iyyar PDP.

Yayin da yake jawabi a wani taro na kungiyar gwamnonin arewa a ranar Alhamis, Umahi ya ce ya koma jam'iyyar APC ne saboda bin zabin Allah da kuma shugaba Muhammadu Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng