Dakarun soji sun dakile bai wa 'yan Boko Haram kudin fansa, sun ragargaza mayakan

Dakarun soji sun dakile bai wa 'yan Boko Haram kudin fansa, sun ragargaza mayakan

- Sojojin Najeriya suna cigaba da samun nasarar ragargazar 'yan Boko Haram da suka yi garkuwa da wasu mutane 5 a Maiduguri

- 'Yan ta'addan sun nemi naira miliyan 2 daga hannun iyalansu, amma sai dai tarkonsu bai kama kurciya ba

- Sojojin sun ceto mutane 5 din, sun kuma kashe daya daga cikin 'yan Boko Haram din, sauran kuma sun tsere da raunika

Rundunar sojin Najeriya suna cigaba da samun nasarar ragargazar 'yan Boko Haram a kauyakun waje-wajen babban birnin Borno, Maiduguri.

Mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar soji, birgediya janar Benard Onyeuko, yace runduna ta 251 ta bataliyar soji ta kaiwa wasu 'yan Boko Haram farmaki a Molai, kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito.

A cewarsa, sai da sojojin suka yi nazari kwarai, kuma suka yi amfani da dabara ta musamman, bayan iyalan wasu mutane da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su sun bukaci Naira Miliyan 2 a hannunsu sun kai musu rahoto.

KU KARANTA: Ina matukar jin kunyar bayyana cewa ni jarumar fina-finai ce, Juliet Njemanze

Kamar yadda takardar tazo: "Cikin kwarewa da dabara, rundunar sojin suka takura wa 'yan Boko Haram a kan su dakata daga amsar kudi daga hannun mutanen."

Dakarun soji sun dakile bai wa 'yan Boko Haram kudin fansa, sun ragargaza mayakan
Dakarun soji sun dakile bai wa 'yan Boko Haram kudin fansa, sun ragargaza mayakan. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan sanda sun bi matar da ta yadda N115,000 ba tare da sani ba, sun kai mata

Ya ce sun fara ragargazar 'yan Boko Haram din, har su ka kashe daya, sauran kuma suka gudu da ciwuka sakamakon harbin da suka sha.

Sojojin sun samu nasarar amso yaran guda 3, tare da mata 2 ba tare da wani abu ya samesu ba. Sannan sun samu bindiga AK47 da wani babur.

A wani labari na daban, a ranar Talata, Umahi ya sanar da sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, bayan 'yan satittuka da aka yi ta rade-radin fitarsa daga jam'iyyar PDP, jaridar The Cable ta wallafa.

Yayin da yake jawabi a wani taro na kungiyar gwamnonin arewa a ranar Alhamis, Umahi ya ce ya koma jam'iyyar APC ne saboda bin zabin Allah da kuma shugaba Muhammadu Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng