Daga zuwa yin itace aka sace ta, sai dawowa gida ta yi da cikin dan Boko Haram

Daga zuwa yin itace aka sace ta, sai dawowa gida ta yi da cikin dan Boko Haram

- Balu Agah ta fuskanci tashin hankali da bala'in kungiyar Boko Haram

- Daga samo itace a daji, 'yan ta'addan suka sace ta, kuma suka gudu da ita

- Da kyar ta gudo, a lokacin tana da tsohon ciki watanni 8, bayan an yi mata fyade

Balu Agah, mai shekaru 25 ta sha wahalar rayuwa. Tana daya daga cikin mazauna sansanin 'yan gudun hijira dake garejin Muna a jihar Borno.

Balu ta je wani daji da yake kusa da su don ta samo itacen da take siyarwa ta samu na tuwo, 'yan boko haram suka kai mata farmaki, HumAngle ta wallafa.

Sun damketa a ranar 1 ga watan Satumban 2019, ana saura kwana 20 babbar sallah. 'Yan ta'addan 19 sun zagayeta, yayin da 5 suke rike da bindigogi, wasu kuma da wukake da adduna.

Sai da suka zane ta kamar bakuwar karya, suna dukanta suna ce mata ta koma ga Allah, hakan ne kadai hanyar tsira. Sun kai ta inda suke ajiye mutane kamar ita, bayan sun umarceta da tayi tsirara don su tabbatar mace ce ita, bayan tafiya ta kwana biyu a kafa da suka yi.

KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 69 ya ce bai taba zuwa asibiti ba don bai taba ciwo ba

A cewarta, an gabatar mata da wani irin abinci mara fasali, wanda dole su ka ci don su rayu. Ta bar 'yan uwanta, mijinta, mahaifinta da yaranta 3, ciki har da jariri mai watanni 7 da take shayarwa. Inda suka rabata da mahaifarta, wato Dowumba, karamar hukumar Mafa, su ka kai ta Burari.

A gaban Balu aka yi wa wata Hauwa yankan rago, bayan ta yi yunkurin guduwa sun kamo ta. Bayan nan suka ja kunnen sauran matan, a kan cewa duk wanda ya kuskura ya gudu, za su yi masa irin hukuncin nan.

Daga zuwa yin itace aka sace ta, sai dawowa gida ta yi da dan mayakin Boko Haram
Daga zuwa yin itace aka sace ta, sai dawowa gida ta yi da dan mayakin Boko Haram. Hoto daga @HumAngle
Asali: Twitter

A cewarta, sun cigaba da tafiya suna wuce kauyuka, har sai da suka isa Bonei, sannan suka gabatar da su a wurin manyansu, wadanda suka ja musu kunnen cewa matsawar su ka bar wata ta gudu, to za su hukunta su.

Sun kawo maza wadanda suka yita zaben mata, idan mace ta ki amincewa a kasheta, idan ta amince a daura aure. Akwai wata yarinya mai shekaru 13, shuwa ce, ita tafi kowa kankanta, sai su ka tura ta dajin Sambisa aka aura wa wani babban dan Boko Haram.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun bi matar da ta yadda N115,000 ba tare da sani ba, sun kai mata

Ita kuma Balu aka aura mata wani Ibrahim, wanda kullum cikin dukanta yake. Ta ce akwai lokacin da ya daketa har sai da hannunta ya kumbura, bayan ta kai kara aka ja masa kunne.

Babban abinda yake kawo fadan shine idan zai kwanta da ita, amma ba ta cigaba da bayani ba, don ba ta so ta tuna.

Bayan ta gaji da zama da mijinta mai cutar da ita, kullum cikin tunanin iyayenta da 'yan uwa, ta yanke shawarar guduwa.

Bayan kwana biyu ta falka da safe ta fara gudu, ta yi iyakar gudun da za ta iya, har sai da ta isa karamar hukumar Dikwa, wacce take 90km da kudancin Maiduguri.

Sai ga ta a sansanin 'yan gudun hijira na garejin Muna a mako na 3 na Augusta, a lokacin tana da tsohon ciki. Kowa ya yi farincikin ganinta, sai dai taji mummunan labarin mutuwar jaririnta.

Bayan komawarta gida ta haifi jaririn Ibrahim, haka nan ta yarda da kaddararta, tana fatan ba zai biyo halin mahaifinsa ba. Ta rada masa suna Abubakar.

Bayan an tambayeta idan za ta sanar masa da yadda aka haife shi idan ya girma, tace Eh, ko bata fada masa ba, wasu za su sanar da shi.

Balu Agah ce mace ta farko da aka tozarta, aka sace sannan aka yiwa fyade lokacin da take kokarin nemo itace a daji.

A wani labari na daban, Wata jarumar fina-finan Nollywood 'yar asalin jihar Imo amma tashin jihar Kano, Juliet Njemanze, ta yi fina-finai masu kayatarwa kamar "Calabash", ta nuna da na saninta na zama jaruma.

Duk da jarumar ta karanta fannin shari'a a jami'a, sannan ta yi suna a harkar fina-finai, amma ta na jin takaicin kyamar da ake nuna mata a matsayinta na jaruma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng