Har yanzu bamu janye yajin aiki ba, muna nan: ASUU

Har yanzu bamu janye yajin aiki ba, muna nan: ASUU

- ASUU ta yi watsi da rahoton cewa ta janye daga yajin aiki

- Kungiyar ta malamai ta fara yaji ne tun watan maris gabanin bullar cutar Korona a Najeriya

Shugaban kungiyar malaman jami'o'i a Najeriya ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemii, a ranar Asabar ya bayyana cewa har yanzu yajin aikin watanni takwas da suka kai na nan daram dam.

Farfesa Ogunyemi ya karyata rahoton cewa ASUU ta janye daga yajin aiki kuma ya jaddada cewa ASUU ba ta shafin Tuwita.

Shugaban ASSU ya bayyana hakan ne ranar Asabar, TVC ta ruwaito.

"ASUU ba ta shafi a Tuwta. Mutane da dama suna damu na da kiraye-kirayen waya kuma na gaji. Idan zamu janye yajin aiki, hira zamu shirya da manema labarai," Ogunyemi yace.

KU KARANTA: Daga komawa APC, gwamna Umahi ya sallami hadimansa 4

Har yanzu bamu janye yajin aiki ba, muna nan: ASUU
Har yanzu bamu janye yajin aiki ba, muna nan: ASUU
Asali: UGC

Mun kawo muku cewa bayan watanni 8 ana muhawara, gwamnatin tarayya ta amince da bukatun kungiyar malaman jami'a ASUU cewa a togaciye mambobinta daga manhajar biyan albashi ta IPPIS.

A zaman da gwamnatin tayi da shugabannin ASUU ranar Juma'a, ta hakura kan wasu lamura wanda ya hada da wajabta biyan malaman ta IPPIS da kuma kar musu kudin alawus da kudin gyaran jami'o'i.

KU KARANTA: Yan bindiga sun budewa mutane wuta kusa da tashar jirgin kasan Kaduna

Amma daga baya Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahotannin da ke cewa an togaciye mambobin kungiyar malaman jami'a ASUU daga manhajar biyan albashin IPPIS har abada.

Ministan Kwadago da aiki, Chris Ngige, ya bayyana cewa an yiwa gwamnati mumunan fahimta ne saboda ba tayi yarjejeniya da ASUU cewa za ta ciresu daga manhajar ba, Vanguard ta ruwaito.

Ya kara da cewa za'ayi amfani da GIFMIS ne na wucin gadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel