Yan bindiga sun budewa mutane wuta kusa da tashar jirgin kasan Kaduna

Yan bindiga sun budewa mutane wuta kusa da tashar jirgin kasan Kaduna

- Ya bindiga sun hallaka matashi daya a harin da suka kai Rigasa Kaduna

- An kai wannan hari ne tsakanin tashar jirgin kasar Abuja-Kaduna da Mando

- Wannan ba shi bane karo na farko da yan bindiga ke budewa mutane wuta a hanyar

Wasu yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kai mumunan farmaki unguwar Rigasa, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna inda suka halaka akalla mutum daya.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro sun yi musayar wuta da yan bindiga har suka gudu misalin karfe 6:15 na yamma.

HumAngle ta samu bayanin mai idon shaida, Musa Lawan, cewa jami'an yan sanda da Sojoji sun dira wajen kuma suka fitittiki yan bindigan.

Ya ce harin ya faru kusa da tashar jirgin kasa dake Rigasa.

Wani mazaunin unguwar wanda ya samu raunin harsashi ya kwanta dama bayan da aka kai shi asibiti.

An bayyana sunan matashin matsayin Rabiu Awwal kuma ya kasance dan fafutukan yaki da rashin tsaro a Arewa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero

Yan bindiga sun budewa mutane wuta kusa da tashar jirgin kasan Kaduna
Yan bindiga sun budewa mutane wuta kusa da tashar jirgin kasan Kaduna Hoto: @shehusani
Asali: Twitter

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa Awwal ya mutu ne sakamakon raunin da ya samu na harsasai.

"Wannan matashin Rabiu Awwal dan yakin fafutukan tabbatar da tsaro a Arewa ne mazauni Kaduna, da yammacin jiya ya rasa rayuwarsa sakamakon raunin bindigan da ya samu yayinda yan bindiga suka kai hari unguwarsa, " Shehu Sani yace

"Za'a yi janaizarsa yau .Inna lillahi wainna Illayhir rajiun, Allah ya jikansa,"

Yan ta'adda masu garkuwa da mutane sun dade suna dakon jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna saboda ita ta kasance hanya daya da mutane ke samun kwanciyar hankalin bi domin gudun hadarin titin Kaduna zuwa Abuja.

KU DUBA: INEC ta haramtawa APC musharaka a zaben maye gurbin kujeran Sanata da za'a yi

A wani labarin kuma, rundunar Ƴan sanda Jihar Katsina ta kama ƴan kungiyar fashi da suke ƙware wurin kashe masu acaɓa bayan sun ƙwace babur ɗin su.

Kakakin ƴan sandan jihar DSP Isah Gambo ne ya gabatar wa manema labarai wadanda ake zargin kamar yadda LIB ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel