INEC ta haramtawa APC musharaka a zaben maye gurbin kujeran Sanata da za'a yi

INEC ta haramtawa APC musharaka a zaben maye gurbin kujeran Sanata da za'a yi

Hukumar gudanar da zaben kasa INEC ta cire jam'iyyar All Progressives Congress APC da dan takarata Peremobowei Ebebi, daga musharaka a zaben kujerar dan majalisan dattawa mai wakiltan mazabar Bayelsa ta yamma.

Shugaban sashen yada labarai na INEC dake Bayelsa, Wifred Ifogah, ya sanar da hakan ranar Alhamis yayinda yake gabatar da jawabi madadin kwamishanan INEC na jihar.

An shirya yin zaben Bayelsa ta tsakiya da Bayelsa ta yamma ne ranar 31 ga Oktoba amma aka dage zuwa 5 ga Disamba sakamakon zanga-zangar #EndSARS.

Ifogah yace hukumar ta yanke shawaran cire APC ne saboda hukuncin babban kotun tarayya dake Yenagoa.

Ya ce kotun ta haramtawa hukumar sanya APC da dan takararta a takardar zabe.

Saboda haka, Ifogah ya ce jam'iyyu 12 kadai za suyi musharaka a zaben.

Babbar kotun tarayya dake Yenagoa karkashin jagorancin Alkali Jane Inyang, a ranar 3 ga Nuwamba ta dakatad da Peremoboei Ebebi na jam'iyyar APC daga takarar zaben kujerar Sanatan Bayelsa ta kudu kan zargin amfani da takardun bogi.

Kotun ta yi watsi da zaben fidda gwanin da ya ci.

DUBA NAN: An garkame Fasto, Uwa da yaro kan kashe daliba tare da cin namarta don kudi

INEC ta haramtawa APC musharaka a zaben maye gurbin kujeran Sanata da za'a yi
INEC ta haramtawa APC musharaka a zaben maye gurbin kujeran Sanata da za'a yi Hoton: @APCNigeria
Asali: UGC

KU KARANTA: Shin da gaske ne Inyamuri 1 kacal ke aiki a fadar shugaban kasa kamar yadda Abaribe yayi ikirari?

Peremoboei Ebebi ya kasance tsohon mataimakin gwamnan jihar.

Amma kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC ta yi alla-wadai da wannan hukunci na INEC inda tace wannan zalunci ne.

Diraktan yakin neman zaben, Offini Williams, ya ce hukumar ya tsunduma cikin siyasa saboda babban kotu ba ita bace kotun koli ba.

A bangare guda, gwamnan Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kaddamar da gidaje 50 da gwamnatin jihar ta gina domin jin dadin kananan ma'aikatan jami'ar Maiduguri.

An fara wannan ginin ne a watan Disamban 2019 kuma yana cikin ayyukan da gwamna Zulum ke yi domin jin dadin yan asaliin jihar Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel