Shin da gaske ne Inyamuri 1 kacal ke aiki a fadar shugaban kasa kamar yadda Abaribe yayi ikirari?

Shin da gaske ne Inyamuri 1 kacal ke aiki a fadar shugaban kasa kamar yadda Abaribe yayi ikirari?

- Shugaban marasa rinjaye a majalisa ya soki Buhari na bangaranci

- Wannan ba shi bane karo na farko da zai zargi Buhari da rashin son kabilarsa ba

- Ya ce wajibi ne dan kabilar Igbo ya gaji Buhari a shekarar 2023

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Eyinnaya Abaribe, ya ce mutum daya dan kabilar Igbo dake fadar shugaban kasa mai daukan hoto ne.

Ya bayyana hakan ranar Juma'a yayinda yake hira a shirin Sunruse Daily na tashar Channels TV.

"Gabanin yanzu, kowace yanki a kasar nan na da wakilci a fadar Aso Villa. Amma yanzu babu kowa (namu) dake cikin Villa. Mutum daya ne kuma sunansa Sunny, ina tunanin mai daukan hoto ne," yace

"Saboda haka (gwamna) Umahi wa zai yiwa magana? Kawai dan shi gwamna ne, zai iya magana da shugaban ma'aikatan Buhari, zai iya ganin shugaban kasa, amma sauran fa?"

KU KARANTA: An garkame Fasto, Uwa da yaro kan kashe daliba tare da cin namarta don kudi

Shin da gaske ne Inyamuri 1 kacal ke aiki a fadar shugaban kasa kamar yadda Abaribe yayi ikirari?
Shin da gaske ne Inyamuri 1 kacal ke aiki a fadar shugaban kasa kamar yadda Abaribe yayi ikirari?
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamna Babagana Umara Zulum ya bude sabbin gidaje 50 da ya ginawa kananan malaman jami'ar UNIMAID

Amma binciken da TheCable tayi cikin ma'aikatan fadar shugaban kasa ya nuna cewa akwai yan kabilar Igbo 9 cikin hadiman shugaba Buhari.

Sune Francis Anatogu, SSA kan lamuran ofishohin gwamnati; Nneka Ikejiani, STA (sashen isa); Somkele Awa-Kalu SA Bahashi; Tochi Nwachuwu (Sashen sayar da wutan lantarki); da Nkechi Chukwueke.

Sauran sune Nkoli Anyaoku, SA DCOS; Nonye Ojekwe, (SA harkokin siyasa); Louisa Chinedu-Okeke, SA Kudi da Juliet Chikaodili-Nwagu, SA sashen shari'a).

Karshe, Sunday Aghaeze da Sanata Abaribe yace dan yankinsu ne, bincike ya nuna cewa dan jihar Delta ne kuma ba dan yankin Kudu maso gabas ba.

Mun kawo muku cewa gwamnonin jam'iyyar APC sun yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, da yammacin ranar Juma'a a Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, wanda ya koma jam'iyyar APC daga PDP kwanan nan; gwamnan jihar Kebbi; Atiku Bagudu, da takwaransa na jihar Jigawa, Abubakar Badaru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng