An garkame Fasto, Uwa da yaro kan kashe daliba tare da cin namarta don kudi
- Wata mahaifiya, danta da fasto sun hallaka dalibar jami'a domin asiri
- Alkali mai shari'a ta bada umurnin garkamesu a kotu har shekarar 2021
Wata kotun jihar Osun ta garkame wata mata, danta da fastonsu kan zargin kashe wata dalibar ajin karshe a jami'ar jihar Legas, Favour Daley-Oladele, tare da cin namansa.
Wadanda aka garkame sune Bola Adeeko, 'danta Owolabi Adeeko, da fastonsu, Segun Philip.
Lauyar gwamnati, Kemi Bello, ce ta kaisu kotu kuma ta caje su da laifin kisan kai.
Amma ba'a karantawa masu laifin zarginsu ba saboda basu da lauya.
Alkali mai shari'a, Grace Onibukun, ta daga karar zuwa ranan 3 da 10 ga Maris, 2020 domin sauraro amma ta yi umurnin a garkamesu a gidan gyara hali.
Za ku tuna cewa hukumar yan sandan jihar Ogun ta damke Faston tare da matar kan kisan daliba Daley-Oladele.
Bayan damkesu, yaron matar, Owolabi, ya bayyana yadda shi da mahaifiyarsa sun hada kai wajen kashe tsohuwar budurwarsa kuma suka girka namanta suka ci domin asirin kudi.
KU KARANTA: Gwamna Babagana Umara Zulum ya bude sabbin gidaje 50 da ya ginawa kananan malaman jami'ar UNIMAID
KU KARANTA: Gwamnatin APC ta fi ta PDP sau dubu - Gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka
A bangare guda, wasu 'yan sanda da 'yan sa kai da ke Ogwashi-Uku, karamar hukumar Aniocha ta kudu da ke jihar Delta, sun kama wasu samari 2 da akwatin gawa, cike da 'yan kamfan mata da rigunan nono.
An kama wadanda ake zargin a wuraren Agidiehe quarters da misalin karfe 9:30 na daren Laraba, kamar yadda labarai suka bayyana.
Sai da 'yan sa kai suka kama su tukunna aka sanar da 'yan sanda. Kamar yadda wata majiya ta sanar, hankulan mata da samarin yankin sun yi matukar tashi sakamakon aika-aikan 'yan damfarar yanar gizon.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng