Da duminsa: Dogarin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bindige mai jarida ba gaira, ba dalili
- Kuma dai, wani dan sanda ya bindige dan kasuwa cikin kure
- Kaakin majalisar wakilai, wanda dogarinsa ya aikata kisan ya bayyana alhininsa
Wani jami'in dan sanda dake gadin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bindige wani mai sayar da jarida a birnin tarayya, Abuja ranar Alhamis.
Kakakin majalisar da kansa ya tabbatar da hakan a shafinsa na Tuwita.
Ya bayyana cewa da yamma bayan tashi daga Ofis, ya tsaya hira da wasu masu sayar da jarida a harabar majalisar dokoki yayinda wasu batagari suka tare motarsa.
Kakakin ya ce hadimansa sukayi harbi sama domin koran batagarin, amma daga baya ya samu labarin cewa harsashi ya samu wani.
Gbajabiamila ya ce wannan abin ya tayar masa da hankali.
"Wani abin takaici ya faru. Da yammacin nan yayinda nike fita daga majalisar dokoki, na tsaya kamar yadda na saba domin gaisawa da masu sayar da jaridun dake kwana. Da yawa cikinsu sun san ni tun lokacin da na dawo Abuja kuma abokai na ne," yace
"Amma, yayinda dogarai na suka karaso wasu matasa sun tare motarmu kuma hakan ya sa daya daga cikin dogaran yayi harbi sama domin tarwatsa su."
"Awanni bayan haka, bayan mun isa idan muka je, na samu labarin cewa harsashi ya samu wani, sabanin bayanin da na samu a baya cewa sama kawai sukayi harbi."
KU DUBA: Mun gano arzikin man fetur mai yawan gaske a wata jihar Arewacin Najeriya, Shugaban NNPC Mele Kyari
KU KARANTA: 2020: Jerin mata 5 da suka fi dukiya a Najeriya da yadda suka tara ta
Tsohon dan takaran shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya bayyana sunan mai jaridan da aka kashe matsayin Ifeanyichukwu Elechi.
A wani labarin kuma, rundunar ƴan sandan Jihar Legas ta yi nasarar kama wani matashi ɗan shekara 19, Ajayi Lateef kan zargin fashi da makami.
An kama shi da bindigar roba bayan ƴan ƙungiyarsu sun yi wa wani mai adaidaita sahu fashi a Victoria Island misalin ƙarfe 1 na dare kamar yadda LIB ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng