2020: Jerin mata 5 da suka fi dukiya a Najeriya da yadda suka tara ta
- Akwai hamshakan masu kudi a fadin Najeriya, wadanda sanannu ne a nahiyar Afirika, da duniya gaba daya
- Dukansu mata ne kuma manya-manyan 'yan kasuwa da kuma 'yan siyasa masu hada-hadar neman na kansu
- A cikin jerin nan za ku ji sunayen mata guda 6 wadanda suka fi duk wasu mata kudi a fadin Najeriya
Allah ya azurta kasar Najeriya da shahararrun masu kudi, kuma 'yan kasuwa. Legit.ng ta yi dubi a kan rayuwar manyan mata masu dukiya 'yan Najeriya.
1. Folorunso Alakija
Alakija babbar 'yar kasuwa ce, wacce ta tara biliyoyin nairori. Yanzu haka, ita ce matar da tafi kowacce mace dukiya a fadin Najeriya, sannan ita ce mace ta biyu a cikin mata masu arzikin nahiyar Afirika.
Matar mai shekaru 69 da haihuwa, ta kasance mai taimako ga gajiyayyu. Sannan ita ce mataimakiyar shugaban Famfa Oil Limited.
KU KARANTA: Bidiyon Emmanuella tana bayanin yadda ta samu kudin gina wa mahaifiyarta katafaren gida
2. Hajia Bola Shagaya
Shagaya ce manajan darektan Practiol Limited, daya daga cikin manyan masu shigo da mai Najeriya.
Ba a dare daya ta tara dukiyarta ba, ta fara ne da aiki a babban bankin Najeriya (CBN) kafin ta fara harkokin kasuwanci a 1983.
3. Daisy Danjuma.
Danjuma lauya ce, wacce ta koma harkar siyasa. Ita ce mace ta 3 a mata masu kudin Najeriya. Ta rike kujerar sanata ta kudancin Edo, tsakanin 2003 zuwa 2007.
Matar mai shekaru 68 ta rike kujerar shugaban SAPETRO. Yanzu haka Daisy tana daya daga cikin 'yan kungiyar lauyoyi na ciki da wajen Najeriya. Daisy tana daya daga cikin hamshakan masu kudin Najeriya.
KU KARANTA: Matashi ya yi wa budurwa mugun duka tare da yunkurin kasheta a kan kudin da ya kashe mata a fitarsu ta farko
4. Fifi Ejindu
Fifi babbar 'yar kasuwa ce, kuma tana sana'ar zanen gidaje. Ita ce mace ta 4 a cikin manyan masu kudin Najeriya.
Yanzu haka tana harkar sayar da man fetur da kuma zane-zanen gine-gine. Hamshakiyar 'yar kasuwa kuma mai taimakon, jika ce ga Sarki James Ekpo Bassey, na garin Cobham da ke jihar Calabar.
5. Dr Stella Okoli
Dr Stella babbar mai hada magunguna ce kuma ita ce mai kamfanin magunguna na Emzor. Mace ce mai yawan taimakon gajiyayyu da mabukata, tana taimaka musu da magunguna da tallafi na harkar lafiya. Ta rike kujerar shugaban MAN. Ita ce mace ta 5 a masu kudin Najeriya mata.
A wani labari na daban, wata mata mai suna Katie Price, ta bayyana yadda take boye abinci don dakatar da jibgegen danta daga mugun ci. A cewarta, har tsakar dare yake tashi yayi ta kwasar abinci yana ci, shiyasa yayi tulele, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Matar mai shekaru 42 ta bayyana yadda babban danta yake bubbula mata bangon dakuna idan ta hana shi cin abinci. Harvey, mai shekaru 18 yana fama da wata cuta, wacce take sa shi yayi ta kwasar gara kamar Allah ya aiko shi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng