Farfesan Likitancin dabbobi na farko a Arewacin Najeriya, Marafan Nupe, ya rasu

Farfesan Likitancin dabbobi na farko a Arewacin Najeriya, Marafan Nupe, ya rasu

- Inna lillahi w ainna ilaihi raji'un

- Arewacin Najeriya ta yi rashin wani babban farfesa cikin farfesoshinta na farko a tariti

- Mai Martaba Etsu Nupe ya yi alhinin mutuwar Farfesa Shehu Jibrin

Farfesan likitancin dabbobi na farko da ya fito daga Arewacin Najeriya kuma tsohon shugaban karamar hukumar Bida a jihar Neja, Shehu Jibrin, ya rigamu gidan gaskiya.

Jibrin wanda shine Marafan Nupe kuma Farfesa na farko da ya fito daga kabilar Nupawa ya rasu ne da safiyar Alhamis a Bida yana mai shekaru 86 bayan gajeruwar rashin lafiya.

Etsu Nupe kuma shugaban sarakunan gargajiyan jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, ya siffancin mutuwar Farfesa Shehu Bida matsayin babban rashi ga al'ummar Nupe, jihar Neja da kuma Najeriya gaba daya.

A cewarsa, marigayin babban malamin Boko ne kuma zakakurin dan siyasa, Daily Trust ta ruwaito.

"Ya kasance Uba mai soyayyar 'yayanda a zuciya. Ya kasance mai tabbatar da zaman lafiya," cewar Etsu Nupe.

KU KARANTA: Dangote, Isyaka Rabiu, da wasu attajirai biyu ne biloniyoyin Najeriya 4 a 2020, Forbes

Farfesan Likitancin dabbobi na farko a Arewacin Najeriya, Marafan Nupe, ya rasu
Farfesan Likitancin dabbobi na farko a Arewacin Najeriya, Marafan Nupe, ya rasu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Fitaccen malami, Sheikh Dahiru Bauchi ya aike wa shugabannin Najeriya muhimmin sako

A wani labarin daban, wani tsohon malamin KADPOLY, mai suna Austin Umera ya shayar da mutane mamaki a kan abinda ya aikata.

Ana zarginsa da laifin harbin matarsa, Dokta Maurin, wacce ita ma malama ce a jami'ar jihar Kaduna (KASU), inda daga bisani ya harbe kansa kuam ya fadi ya mutu.

Al'amarin ya faru ne a gidansu da ke layin Kigo a cikin garin Kaduna. Yanzu haka Dokta Maurin tana kwance a asibitin sojoji na 44 da ke cikin Kaduna, inda ake cigaba da kulawa da lafiyarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel