Innalillahi: Tsohon malami a KADPOLY ya harba matarsa tare da kashe kansa
- Ana zargin wani tsohon malamin KADPOLY da kashe kansa
- Sai da Austin Umera ya harbi matarsa, sannan ya kashe kansa
- Har yanzu ba a gano dalilin da zai sa babban mutum irinsa ya kashe kansa ba
Wani tsohon malamin KADPOLY, mai suna Austin Umera ya shayar da mutane mamaki a kan abinda ya aikata.
Ana zarginsa da laifin harbin matarsa, Dokta Maurin, wacce ita ma malama ce a jami'ar jihar Kaduna (KASU), inda daga bisani ya harbe kansa kuam ya fadi ya mutu.
Al'amarin ya faru ne a gidansu da ke layin Kigo a cikin garin Kaduna.
Yanzu haka Dokta Maurin tana kwance a asibitin sojoji na 44 da ke cikin Kaduna, inda ake cigaba da kulawa da lafiyarta.
An adana gawar mijinta a ma'adanar gawa dake asibitin kwararru na Barau Dikko a Tudun wada.
Jaridar Daily Trust ta samu labarin wannan mummuna al'amarin ne da misalin karfe 10 na daren Laraba.
Har ila yau, babu cikakke kuma gamsasshen bayani a kan silar aukuwa lamarin amma kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin.
KU KARANTA: Matashi ya yi wa budurwa mugun duka tare da yunkurin kasheta a kan kudin da ya kashe mata a fitarsu ta farko
KU KARANTA: Hotunan budurwar da tsohon kwamishinan dan sanda ya fizge wa kunne da cizo
A wani labari na daban, kowa yana da ra'ayi da zabi idan aka zo batun soyayya, amma yawancin mutane su kan duba aljihu.
Wata budurwa, mai suna Rutie, ta janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, bayan ta bai wa matasa shawara a kan soyayya.
Kamar yadda Rutie ta ce, duk saurayin da bashi da a kalla naira miliyan 25 a asusunsa, bai dace da soyayya ba.
Nan da nan samari da 'yan mata suka yi ta tururuwa suna yin tsokaci a karkashin wallafar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng