Fitaccen malami, Sheikh Dahiru Bauchi ya aike wa shugabannin Najeriya muhimmin sako

Fitaccen malami, Sheikh Dahiru Bauchi ya aike wa shugabannin Najeriya muhimmin sako

- Shugaban kungiyar Tijjaniyya ta Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya shawarci shugabanni da su kasance masu adalci

- Sheikh Bauchi ya kara da shawartar matasa da su yi biyayya ga shugabanni da kuma dokokin addininsu don samun zaman lafiya

- Malamin ya yi wannan jawabin ne a wani taro a Abuja, wanda ANEST da Blue Bells Promoters suka shirya, wanda manyan mutane suka halarta

Wani babban malamin musulunci, kuma shugaba ga kungiyar musulmai ta Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya roki 'yan siyasa da shugabannin addini da ke cikin Najeriya da su ji tsoron Allah su tabbatar da adalci, su kuma cire banbancin addini ko al'ada tsakanin wadanda suke jagoranta.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan maganar ne a Abuja, a wani taro, wanda aka dauki bidiyonsa mai taken Lisanul Faidha wato Muryar Musulunci, wanda ANEST da Blue Bells Promoters suka shirya.

Kamar yadda Sheikh Bauchi yace, "Ubangiji ya umarci duk wani shugaba tun daga gidaje, anguwanni, kananun hukumomi, har zuwa shugaban kasa da su kasance masu tabbatar da kwatanta adalci tsakanin mabiyansu don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali."

Ya kuma shawarci masu wa'azi da su tabbatar sun samar da zaman lafiya da juriya ta addinai mabambanta, Daily Trust ta wallafa.

Ya shawarci matasa da su nemi ilimi, domin ilimi shine gishirin zaman duniya, kuma shine kadai zai samar da cigaban al'umma.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya roki matasa da su yi kokarin bin shawarar da Sheikh Bauchi ya bayar da kuma biyayya ga dokokin addinin musulunci.

KU KARANTA: Bidiyon Aku a wata liyafa, yana kwasar wata rawa mai bada mamaki

Fitaccen malami, Sheikh Dahiru Bauchi ya aike wa shugabannin Najeriya muhimmin sako
Fitaccen malami, Sheikh Dahiru Bauchi ya aike wa shugabannin Najeriya muhimmin sako. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Sabbin mutum 152 sun sake kamuwa da cutar korona a Najeriya

A wani labari na daban, wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP na yankin kudu maso gabas sun yi ikirarin barin jam'iyyar matukar APC bata tsayar da 'dan takarar shugaban kasa daga yankinsu ba.

Shugabannin PDP sun lashi takobin ba za su bari dan bangarensu ya zauna a matsayin mataimakin shugaban kasa ba, kuma za su dauki duk wanda ya amshi matsayin mataimakin shugaban kasa a matsayin makiyin yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng