An haifi yaro da mazakuta biyu a babban asibitin yara dake kasar Masar

An haifi yaro da mazakuta biyu a babban asibitin yara dake kasar Masar

- Ikon Allah ba ya karewa, an haifi wani irin jariri da ba'a taba gani ba a kasar Masar

- Ana bukatan kwararrun Likitocin da zasu yiwa jaririn aiki bayan ya cika shekara 1 da yan watanni

An haifi wani yaro da mazakuta biyu sakamakon rashin girman dan'uwansa cikin mahaifa, Likitoci sun yi bayani.

Wannan abin al'ajabi, da aka wallafa a mujallar IJS, ya nuna yadda aka haifi yaron da al'aura biyu, mafitsara biyu ta yadda zai iya fitsari ta hanyoyin biyu.

Mawallafin rahoton, Ahmed Maher Ali, da tawagar Likitocinsa na asibitin yaran jami'ar Assiut, a Masar, yace: "Wannan karon akwai mazakuta biyu, kowanne da 'yayan gwalakensa."

Rahoton ya kara da cewa: "Mun gabatar da wani sabon jariri mai mazakuta biyu da mafitsara biyu."

"Wannan na da muhimmaci saboda sabon ilimi ne da muka gano."

"Bamu san abin da ya sabbaba wannan ba, masana sun yi kokarin bayaninsu amma wanda yake kusa da gaskiya shine yan biyu aka so haifa ammam suka rabu."

"Wannan wani abu ne dake da wuyan faruwa kuma ana bukatan zakakuran masana domin gyara mazakutar."

"Muna shirin fara yi masa aiki yana kaiwa watanni 16 da haihuwa."

A cewar Science Direct, haifan yaro da mafitsara biyu abune dake faruwa sau daya cikin jarirar milyan biyar.

KU KARANTA: Ranar 3 ga Disamba zamu kammala aiki kan kasafin kudin 2021, Majalisar dattawa

An haifi yaro da mazakuta biyu a babban asibitin yara dake kasar Masar
An haifi yaro da mazakuta biyu a babban asibitin yara dake kasar Masar
Asali: Facebook

A wani labarin daban, an kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa mai suna Ruqayya Rabi'u a Jigawa bayan samun ta da jabun kuɗade (dubu ɗai-dai guda 100 da ɗari biyar-biyar guda 76) a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Wacce ake zargin dai ƴar asalin ƙaramar hukumar Bichi ne a Kano ta shiga hannu ne bayan ta siya man shafawa na N300 a kasuwa kamar yadda LIB ya ruwaito.

Madogara: Mirror News

KU KARANTA:FG ta saki N5.2bn domin ginin gidajen 'yan gudun hijira, Zulum

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng