Wadanda suka sace mutane 5 yan gida daya a Abuja sun bukaci N30m kudin fansa
- Masu garkuwa da mutane suna cin karensu ba babbaka a birnin tarayya Abuja
- Bayan harin da suka kai Tunga-Maje, sun yi awon gaba da mutane a Kuje
- Wadanda aka dauke wannan karon duk yan gida daya ne kuma suna neman miliyoyi kudin fansa
Masu garkuwa da mutanen da sukayi awon gaba da mutane biyar yan gida daya a unguwar Pengi na garin Kuje a birnin tarayya Abuja sun ce wajibi ne a biyasu N30 million kudin fansa kafin su sakesu.
Wani rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa an sace wasu ƴan gida ɗaya su biyar a garin Pegi da ke ƙaramar hukumar Kuje a Abuja.
A cewar rahoton, wadanda aka yi garkuwa da su sun hada da Jubril Abdullateef (22), Sherifat Abdullateef (20), Muyidat Abdullateef (13) Nura Abdullahi (18) da Nahimat Abdullahi (9).
Wani dan'uwan wadanda aka sace, wanda aka sakaye sunansa, ya ce sun samu nasarar tattaunawa da masu satan mutanen lokacin da suka kira domin bukatan kudin fansa.
A cewarsa, masu garkuwan sun yi amfani da wayar hannun da suka kwace daga hannun mahaifiyar yara 5 da suka sace, Latifat Abdullateef, wajen kiransu.
"Iyalin sun samu nasarar tattaunawa da masu garkuwa da mutanen da yammacin Laraba, kuma sun bukaci milyan 30 kafin su sakesu, amma har yanzu ana tattaunawa, " yace.
Kakakin hukumar yan sanda birnin tarayya, ASP Maryam Yusuf, ba ta daga wayarta ko amsa sakonninta ba domin tabbatar da gaskiyar bukatar masu garkuwan.
KU KARANTA: Ranar 3 ga Disamba zamu kammala aiki kan kasafin kudin 2021, Majalisar dattawa

Asali: UGC
KU KARANTA: FG ta saki N5.2bn domin ginin gidajen 'yan gudun hijira, Zulum
Mun ruwaito muku cewa wani makwabcinsu yace ƴan bindigan sun kwashe kimanin minti 20 ba tare da yin harbi ba sannan suka tsere da yaran kafin ƴan sanda da sojojin ruwa da ke kusa da unguwar su iso.
Kakakin kungiyar cigaban Pegi, Oyedeji Oyetunji ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce;
"Abinda muke fuskanta a Pegi shine wasu ƴan bindiga sun shiga gidan maƙwabtan mu sun sace ƴan gida ɗaya su biyar."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng