'Yan bindiga sun kashe jami'an sintiri uku a Kaduna, in ji Hukuma

'Yan bindiga sun kashe jami'an sintiri uku a Kaduna, in ji Hukuma

- Jami'an sintiri uku sun rasa rayukansu a hannun yan bindiga a jihar Kaduna

- Gwamnan jihar Nasiru El-Rufai ya mika ta'aziyyar sa ga iyalan wanda abin ya shafa

- El-Rufai ya yabawa sojoji kan samun nasarar ragargazar wasu 'yan ta'adda a jihar

Jami'an sintirin jihar Kaduna (KADVIS) sun gamu da ajalinsu yayin arangama da yan bindiga a karamar hukumar Chikun, da yammacin Talata, a cewar wani jami'i.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka ranar Laraba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

'Yan bindiga sun kashe jami'an sintiri uku a Kaduna, in ji Hukuma
'Yan bindiga sun kashe jami'an sintiri uku a Kaduna, in ji Hukuma. Hoto daga @channelstv
Asali: UGC

Ya kuma ce daga baya sojoji sun yi nasarar kashe yan tawayen da suka kaiwa jami'an hari, a kauyen Dande a babban garin Bukuru.

"Jami'an sun kuma lalata maboyar yan tawayen dake yankin," a cewar sa.

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Kwamishinan ya bayyana sunayen jami'an a matsayin Alison Musa, Dauda Audu da Ishaya Sarki.

Ya ce ragowar mutum biyu, Ayuba Tanko da Doza Adamu sun ji rauni.

Mr Aruwan ya kuma ce gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya mika ta'aziyya ga iyalan wanda abin ya shafa.

"Gwamnan ya yabawa sojojin sama dana kasa na "Operation Thunder Strike" a wani atisaye da suka sami nasara a yakin Kuku, a karamar hukumar Kagarko a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

KU KARANTA: Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun Halima Nwakaego sun janyo masa caccaka

"Gwamnan ya ce ya samu kyakkyawan labarin cewa harin sama na farko an samu nasarar rushe wasu gine gine da kuma halaka wasu yan bindiga.

"Sannan a hari na biyu da jirage masu saukar ungulu na rundunar sojin sama da suke bawa jami'an rundunar sojojin kasa kariya a ci gaba da atisayen daga Kagarko zuwa Kuku inda maboyar yan tawayen take."

A wani labarin, bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel