Duba kyaututtuka 30 da budurwa ta gwangwaje saurayinta da shi a ranar zagayowar haihuwarsa

Duba kyaututtuka 30 da budurwa ta gwangwaje saurayinta da shi a ranar zagayowar haihuwarsa

- Salon bayyana soyayya sune a baki da kuma ayyuka, tsakanin masoya

- Wata budurwa ta shayar da masoyinta mamaki a ranar zagayowar haihuwarsa

- Ta gabatar da kyautukan, ana saura kwana 30 ya cika shekaru 30, don kullum ya bude daya har ranar haihuwarsa

Soyayya ruwan zuma, wasu kuma su kan ce ruwan madaci, ko ma dai wannene, wannan budurwa ta zurfafa soyayyarta ga saurayinta.

Wata budurwa mai karancin shekaru ta nuna wa duniya soyayyar da take yi wa saurayinta.

Budurwar wani mai amfani da TheJamelShow, a shafinsa na Twitter, ta shayar da saurayinta mamaki a ranar zagayowar haihuwarsa ta 30, wacce zata zo nan da wata daya.

Bidiyon ya nuna budurwar tana tafiya a wani daki wanda ta jere duk kyautukan a wani bangare na dakin. Duk ta rufe kyautukan cikin kwalaye. Ta kuma jera kofuka 30.

A cewarta, kullum sai ya sha daga kowanne kofi kafin ya bude kowacce kyauta, sannan zai yi hakan kowacce rana, na kwanaki 30.

Saurayin ya kasa yarda da cewa ba mafarki yake yi ba, shine saurayin ya wallafa a shafinsa na Twitter, @TheJamelShow.

KU KARANTA: Abinda yasa magidanci ya banka wa budurwarsa wuta ta kone kurmus a Benue

Duba kyaututtuka 30 da budurwa ta gwangwaje saurayinta da shi a ranar zagayowar haihuwarsa
Duba kyaututtuka 30 da budurwa ta gwangwaje saurayinta da shi a ranar zagayowar haihuwarsa. Hoto daga @TheJamelShow
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna

A wani labari na daban, bidiyon wani dan sandan kasar Ghana ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wanda aka ga wani dan sanda wanda direba ya bai wa rashawa ya ki amsa, kuma ya ja kunnensa a kan kada ya maimaita.

Har yanzu ba a samu sunan direban ba, amma alamu sun nuna dan yankin Volta ne, mazaunin anguwar Akan, saboda yanayin yadda yake magana a yaren Twi, da harshen Ewe.

A bidiyon, dansandan ya dakatar da wata mota mai suna 'Mahama Camboo' don ya dudduba, The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel