An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi

An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi

- Mutumin nan da yayi tattaki daga Gombe zuwa Abuja saboda taya Buhari murna ya more

- Gwamnan jihar Gombe ya gwangwaje Buba dan karamar hukumar Dukku da mota da Naira miliyan 2

- Dattijon mai shekaru 50, wanda dama direba ne, ya shiga cikin matsanancin farin ciki

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya gayyaci Dahiru Buba zuwa masaukin gwamnan da ke Abuja a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2020, Channels TV ta wallafa.

Dahiru Buba, mutumin da yayi tattaki daga jihar Gombe har Abuja don taya murnar nasarar Buhari a 2015, ya samu kayan alatu daga hannun gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya.

Rahotanni sun nuna yadda Buba ya kwanta asibiti kwanaki sakamakon ciwon kafar da ya fuskanta.

Ciwon kafar da ake zargin tattakin ne yayi sanadinshi, bayan Buba ya fara neman taimako ne gwamnan ya bukaci a kai shi babban asibiti don samun kulawa ta musamman.

Warkewarsa ke da wuya, gwamnan ya gayyaceshi Abuja, inda yayi masa kyauta ta musamman don taimakonsa.

Tsohon, dan karamar hukumar Dukku, wanda dama direba ne, yayi matukar farincikin samun kyauta mai tsoka daga hannun gwamnan a ranar Litinin, inda gwamnan ya bashi dalleliyar mota da kuma naira miliyan 2.

An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi
An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannuwa ana kashesu kamar kaji ba, kwamishina

An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi
An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi
An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yar hidimar kasa ta haihu a sansanin bautar kasa da ke Ekiti

An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi
An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

A wani labari na daban, Allah mai halitta iri-iri, wasu masu kiba, wasu sirara, wasu kuma dogaye wasu gajeru. Cardoso Oluwatosin Michael, dan jihar Lagos bai dade da gama bautar kasarsa ba a Minna, jihar Niger.

Cardoso ya gama karatunsa a Polytechnic din jihar Ibadan, inda yayi karatu a kan harkokin gwaje-gwajen asibiti a 2018.

Yanzu yana shirin samun mata ne ya aura, wacce za su wuce kasar waje don ya cigaba da karatunsa. Sai dai yana da wata matsala.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel