Gwamnan Kogi ya ziyarci Buhari, ya mika wata muhimmiyar bukatar jiharsa gabansa
- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya je fadar shugaban kasa, inda ya roki a gina filin jirgin sama a jiharsa
- Gwamnan ya tattauna yuwuwar fadada kogin Neja har zuwa Lokoja don bubbugo da tattalin arzikin arewa
- A cewar gwamnan, yana kyautata zaton gina filin jirgin zai bunkasa tattalin arzikin arewa, da Najeriya gabadaya
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka ta gina tashar jirgin sama a jiharsa kuma ta fadada kogin Neja har zuwa Lokoja, don bubbugo da tattalin arzikin jihar da Najeriya gabadaya.
Ya bayyana wa manema labaran cikin fadar shugaban kasa hakan a ranar Talata, bayan taron da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Kamar yadda yace, "Na ziyarci shugaban kasa, inda na gabatar masa da bukatun jihata da kuma matsalolin da muke fuskanta. Na isar masa da sakon mutanen jihar Kogi, saboda alaka mai karfi da ke tsakaninsu da gwamnati.
"Na kuma roki shugaban kasa a kan bukatar mu ta samun filin jirgin sama a jihar Kogi, kafin a saki kudade, don a fara duba jihar Kogi.
"Na kuma janyo hankalin shugaban kasa a kan fadada kogin Neja har zuwa Lokoja, har zuwa Baro idan zai yuwu. Muna bukatar bubbugo da tattalin arzikin arewa da Najeriya gabadaya.
KU KARANTA: An gwangwaje mutumin da yayi wa Buhari tattaki da kyautar mota da makuden kudi
KU KARANTA: 'Yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannuwa ana kashesu kamar kaji ba, kwamishina
A wani labari na daban, majalisar tarayya, kwamitin kungiyar yakin neman zaben Buhari na 2019, ta musanta zargin adana kayan tallafin COVID-19 da aka bada don raba wa 'yan Najeriya.
A cewar majalisar, babu wani sanata da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa kudi ko kuma kayan tallafin COVID-19, Vanguard ta wallafa.
Sun gode wa shugaban kwamitin yada labarai da kamfen din Buhari, Engr. Kailani Muhammad, da yayi gaggawar sanar da su abinda ake ciki, inda suka ce babu wani dan majalisa da aka bai wa kayan tallafin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng