Hotunan motocin alfarma da Regina Daniels take hawa tun bayan aurenta da Ned Nwoko

Hotunan motocin alfarma da Regina Daniels take hawa tun bayan aurenta da Ned Nwoko

- Hakika kudi yana fitar da mutum daga cikin halin kaskanci zuwa daukaka, kuma mata da dama za su iya auren mai kudi ko a mata ta nawa za su zama

- Regina Daniels, kyakkyawar jarumar fina-finan Nollywood, wacce ta auri biloniya a matsayin matarsa ta 6 tana more rayuwa

- Kyakkyawar jarumar, mai shekaru 16 da haihuwa ta nuna kaunar tsadaddun motoci tun bayan auren mashahurin mai kudin

Regina Daniels tana daya daga cikin manyan jaruman Nollywood kuma sanannu, tana da a kalla mutane miliyan 8 da suke bibiyar shafukanta na kafafen sada zumuntar zamani, kamar Instagram.

Kama daga sanda ta fara harkar fim, har zuwa aurenta da mashahurin biloniyan nan kuma sananne, Ned Nwoko, da haihuwar santalelen jaririnta, Munir, mutane su na ta bibiyar rayuwarta.

Tun bayan auren biloniyan nan, Regina ta zage wurin nuna kaunar motocin kece raini.

Hotunan motocin alfarma da Regina Daniels take hawa tun bayan aurenta da Ned Nwoko
Hotunan motocin alfarma da Regina Daniels take hawa tun bayan aurenta da Ned Nwoko. Hoto daga Reginadaniels
Asali: Instagram

Jaridar Legit.ng ta tattaro ire-iren motocin da Regina ta fara hawa na alatu tun bayan aurenta.

1. Lamborghini

Regina ta nuna yadda take kaunar motoci masu kayatarwa da tsada a lokuta daban-daban. A wani bidiyo, wanda ta wallafa a Instagram, tana tuka mota a kan titi, yayin da ta saka wakar Timaya, wanda take cikin Lamborghini.

2. Mercedes Benz Matic

An ga Regina, mai shekaru 16 da haihuwa ta dauki hotuna a cikin motar, wacce kudinta ya zarce naira miliyan 20.

KU KARANTA: 'Yan sanda ba za su cigaba da kalmashe hannuwa ana kashesu kamar kaji ba, kwamishina

3. Ferrari

Regina ta dauki hotuna da dama a gefen wata mota kirar Ferrari, wacce manyan masu kudi suke burin mallaka.

4. Brabus Adventure Mercedes Benz G Wagon

Ga dukkan alamu, jarumar ta fi son motar, domin tana yawan yin hotuna a gefenta. Ita ce motar da mijinta ya bata da hannunsa.

KU KARANTA: Bani da budurwa saboda mata suna tsoron tsayi na, matashi mai kammala hidimar kasa

5. Roll Royce

6. VIP Bus

Wannan ita ce motar da mijinta ya bata, a matsayin kyautar ranar zagayowar haihuwarta.

A wani labari na daban, an gano cewa mijin Regina Daniels, wacce ta bar kyakkyawan saurayinta ta auri tsohon biloniya kuma dan siyasa, Ned Nwoko, yana shirin kara aure.

An saka ranar auren Ned Nwoko da wata hadaddiyar budurwa mazauniyar Ingila, a matsayin matarsa ta 7.

Budurwar mai suna Sara, mai amfani da suna 'Sar8al' a kafar sada zumunta ta Instagram, ta zo Najeriya inda tayi 'yan kwanaki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel