Ba zan sake lamuntan irin zanga-zangar EndSARS ba: Buhari ga majalisar tsaro

Ba zan sake lamuntan irin zanga-zangar EndSARS ba: Buhari ga majalisar tsaro

- Shugaba Buhari ya shiga ganawar sirri da majalisar tsaron tarayya

- Ministan harkokin yan sanda, Muhammad Dingyadi, ya laburtawa manema labarai abinda suka tattauna

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai sake bari zanga-zanga irin ta #EndSARS ta maimata kanta a Najeriya ba.

A ganawar da yayi majalisar da tsaron tarayya ranar Talata, ya ce za'a dama da "masu ruwa da tsaki da matasa wajen kiyaye aukuwar irinta nan gaba, Sun ta ruwaito.

Ministan harkokin yan sanda, Muhammad Dingyadi, ya bayyana hakan yayin hira da manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawarsu da shugaba Buhari a a Villa.

A cewar Dingyadi, an shirya zaman ne domin sanar da Buhari halin tsaron da kasar ke ciki.

Akan zanga-zanga kuwa, yace: "Shugaban kasa ya tabbatarwa yan Najeriya cewa zai yi dukkan abin da zai yiwu wajen tabbatar da cewa zanga-zangar EndSARS bata maimaita kanta a Najeriya ba."

"Shugaban kasan ya tabbatarwa masu ruwa da tsaki cewa za'a dama da kowa, musamman matasa, sarakunan gargajiya, ma'aikatan gwamnati, da malaman addini, wajen tabbatar da zaman lafiya."

Ba zan sake lamuntan irin zanga-zangar EndSARS ba: Buhari ga majalisar tsaro
Ba zan sake lamuntan irin zanga-zangar EndSARS ba: Buhari ga majalisar tsaro Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel