Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga kauyen Kaduna, sun kwashe mutum 11

Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga kauyen Kaduna, sun kwashe mutum 11

- 'Yan bindiga sun kashe akalla mutane 11 a wani sabon hari da suka kai kauyen Kaduna

- Da misalin karfe 1 na ranar Litinin, 'yan ta'addan suka bude wa mazauna kauyen Albasu wuta

- Kwamishinan tsaron ciki da harkokin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar Lamarin

A kalla mutane 11 'yan bindiga suka kashe a sabon harin da su ka kai kauyen Albasu a Sabon Birni, karkashin karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna, Channels TV ta wallafa.

'Yan bindigan sun je ne da yawansu, inda suka afka wa kauyen da misalin karfe 1 na ranar Litinin.

Sun bude wa mazauna kauyen wuta ta ko ina, sanadiyyar haka suka yi ajalin mutane da dama, sun kwashe shanaye da dabbobi masu yawa na kauyen.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Sunday Aruwan ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace an bi bayan 'yan ta'addan da nufin kama su.

Ya kuma bayyana yadda aka yi garkuwa da wasu mutane 2, sannan aka kashe 1 a Maraban Kajuru da ke karamar hukumar Kajuru a ranar Lahadi.

Ya kara da cewa, Gwamna Nasir El-Rufai, ya tura da sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda al'amarin ya shafa, da kuma fatan Allah yayi musu rahama.

KU KARANTA: Ndume: Buhari na zagaye da manyan barayi a mulkinsa

Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga kauyen Kaduna, sun kwashe mutum 11
Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga kauyen Kaduna, sun kwashe mutum 11. Hoto daga @ChannelsTv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugabancin kasa a 2023: PDP na fuskantar babban kalubale a kudu maso gabas

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna tace wata Rundunar Operation Thunder Strike ta samu nasarar ceto wasu mutane 9 da masu garkuwa da mutane suka sace a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadi da rana.

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da hakan ne ta wata takarda, wacce ta fito daga wurin Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel