Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna

Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna

- Rundunar sojoji ta Operation Thunder strike sun samu nasarar ceto mutane 9 daga hannun masu garkuwa da mutane

- Kamar yadda kwamishinan tsaro, Sunday Aruwan ya shaida, bayan rundunar ta bi sahu ne a ranar Lahadi da rana hakan ya auku

- Rundunar ta samu labarin yadda 'yan bindiga suka toshe titin Kaduna zuwa Abuja, tana isa wurin ta fara musayar wuta da su

Gwamnatin jihar Kaduna tace wata Rundunar Operation Thunder Strike ta samu nasarar ceto wasu mutane 9 da masu garkuwa da mutane suka sace a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadi da rana.

Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna
Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna. Hoto daga @MG_Maigamo
Asali: Twitter

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da hakan ne ta wata takarda, wacce ta fito daga wurin Samuel Aruwan, kwamishinan harkokin tsaron cikin gida.

Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna
Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna. Hoto daga @MG_Maigamo
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan 'yan Boko Haram da soji suka kashe, sun damke mai hada bama-bamai a Borno

Kamar yadda takardar ta zo: "Rundunar Operation Thunder Strike ta fita sintiri wuraren Akilubu- Gidan Busa a hanyar Kaduna zuwa Abuja, bayan an sanar da su cewa wasu 'yan bindiga sun dakatar da babban titi, da misalin karfe 4.

Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna
Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna. Hoto daga @MG_Maigamo
Asali: Twitter

"Sun bude wa wata mota wuta, inda suka dakatar da motar. Bayan isar sojojin wurin da abin ya faru ne suka gano ashe har 'yan bindigar sun yi garkuwa da mutane 9 a wata mota mai mazaunin mutane 18, mai lamba ta Kaduna: MKA-151.

Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna
Hotuna: Dakarun soji sun ceto mutum 9 daga hannun 'yan bindiga a Kaduna. Hoto daga @MG_Maigamo
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda budurwa dauka matashi mai talla a titi, ta sauya masa rayuwarsa gaba daya

Take a nan rundunar ta bibiyi 'yan ta'addan suka fara harbin juna, garin hakan ne ta samu nasarar ceto mutane 9, wadanda daga baya suka koma mota tare da abokan tafiyarsu.

Sai dai, direban motar da kuma mai zama gefensa sun rasa rayukansu. Gwamnatin jihar Kaduna tana mika sakon ta'aziyyar ta ga 'yan uwansu.

A wani labari na daban, samamen da dakarun sojin kasar nan ke cigaba da kaiwa yana matukar tasiri a yankin arewa maso gabas na kasar nan. Sun yi nasarar damke wasu masu hada bama-bamai.

Wannan nasarar na kunshe ne wata takardar da hedkwatar tsaro ta kasa ta fitar a ranar Lahadi wacce Birgediya Janar Benard Onyeuko yasa hannu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel