Bidiyon Aku a wata liyafa, yana kwasar wata rawa mai bada mamaki

Bidiyon Aku a wata liyafa, yana kwasar wata rawa mai bada mamaki

- Kafafen sada zumuntar zamani sun dauki zafi bayan ganin wani bidiyon aku yana kwasar rawa

- A bidiyon an hangi akun yana cashewa bayan ya fara jin sautin waka yana tashi

- Mutane da dama sun yi ta mamakin yadda dabba irin aku har ya san sauti

Mutane da dama suna cewa aku tana yin abubuwan da 'yan Adam suke yi. A wani bidiyo, wanda fiye da mutane 200,000 suka duba, an ga tsuntsun yana kwasar rawa.

Yayin da aka fara saka waka, tsun-tsun ya lura da yanayin yadda mutane suke rawa, sai ya fara kwaikwaya.

Sannan akun ya cigaba da bin sautin wakar, yana kwasar rawa. An dauki bidiyon tsuntsun yana cashewa, inda aka yi ta yada shi, jama'a suna shan mamaki.

A cikin tsuntsaye, Aku ne kadai yake iya magana ta hanyar kwaikwayon jama'a.

KU KARANTA: Saurayi ya halaka abokin takararsa wurin neman soyayyar budurwa a Bauchi

Bidiyon Aku a wata liyafa, yana kwasar wata rawa mai bada mamaki
Bidiyon Aku a wata liyafa, yana kwasar wata rawa mai bada mamaki. Hoto daga @cctv_idiot
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kayatattun hotunan bikin dan Tambuwal, ministoci, gwamnoni da masu hannu da shuni sun halarta

A wani labari na daban, tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta kudu, Dino Melaye, ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani bayan ya saki bidiyonsa yana kwasar rawa a tsakiyar hamada.

An san sanatan da nishadantar da mabiyansa da wakoki da raye-raye masu burgewa. Kuma yana wallafa su ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

An ga tsohon sanatan a hamada tare da wasu larabawa yana kwasar rawa. Mutane da dama sun je kasan wallafar tasa suna tofa albarkatun bakinsu.

Wata bennylyon1 cewa tayi: "Kada mutum ya kuskura ya bar kunci da takaici su dame shi, hasali ma, farinciki da nishadi shi yafi."

Wani IcePrint2 yace: "Muna fatan Ubangiji yayi maka jagora. Mu masu kaunar ka ne har abada."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel