Hotunan 'yan Boko Haram da soji suka kashe, sun damke mai hada bama-bamai a Borno

Hotunan 'yan Boko Haram da soji suka kashe, sun damke mai hada bama-bamai a Borno

- Dakarun sojin Najeriya suna samun manyan nasarori a yaki da ta'addanci a yankin arewa maso gabas na kasar nan

- A wani samame na musamman da dakarun suka kai, sun samu nasarar halaka mayakan ta'addancin masu tarin yawa

- Sojojin sun samu nasarar damke kwararru wurin hada bama-bamai wadanda mayakan ke amfani da su

Samamen da dakarun sojin kasar nan ke cigaba da kaiwa yana matukar tasiri a yankin arewa maso gabas na kasar nan. Sun yi nasarar damke wasu masu hada bama-bamai.

Wannan nasarar na kunshe ne wata takardar da hedkwatar tsaro ta kasa ta fitar a ranar Lahadi wacce Birgediya Janar Benard Onyeuko yasa hannu.

Ya ce da yawa daga cikin mayakan ta'addancin sun sheka lahira bayan samame da ruwan wutan da rundunar Opertaion Lafiya Dole suka musu.

Kamar yadda takardar ta fitar, rundunar dakarun sojin sun samu wannan nasarar ne a ranar 11 ga watan Nuwamban 2020.

Bataliya ta 151 ta sojoji na musamman da ke yankin Miyanti sun yi aiki da bayanan sirri inda suka tarwatsa maboyar 'yan ta'addan da ke kauyen ladantar.

Hotunan 'yan Boko Haram da soji suka kashe, sun damke mai hada bama-bamai a Borno
Hotunan 'yan Boko Haram da soji suka kashe, sun damke mai hada bama-bamai a Borno. Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tubabben dan Boko Haram ne ya bai wa 'yan ta'adda sirrin soji a harin Damboa, Ndume (Bidiyo)

Hotunan 'yan Boko Haram da soji suka kashe, sun damke mai hada bama-bamai a Borno
Hotunan 'yan Boko Haram da soji suka kashe, sun damke mai hada bama-bamai a Borno. Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Hotunan 'yan Boko Haram da soji suka kashe, sun damke mai hada bama-bamai a Borno
Hotunan 'yan Boko Haram da soji suka kashe, sun damke mai hada bama-bamai a Borno. Hoto daga @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan Dino Melaye yana kwasar rawa a hamada ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike ta samu nasarar kashe wasu 'yan ta'adda da suke dauke da miyagun makamai.

'Yan ta'addan suna tafe ne a babura tare da shanu da tumakai a kauyukan Dankolo da Machitta da ke jihar Kaduna.

Rundunar sojin saman sun hangi 'yan ta'addan ta wata na'ura mai hangen nesa, inda suka hangi 'yan ta'addan a kauyen Kaboru, suna tunkarar dajin Kwiambana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel