Mata sun fi kasancewa cikin farin ciki ba idan basu tare da maza, Jaruma Inem
- Fitacciyar jarumar fina-finan masana'antar Nollywood, Inem Peter, ta ja wa kanta suka
- Kamar yadda jarumar ta wallafa, ta ce mata sun fi zama cikin farin ciki idan basu tare da maza
- Jarumar ta kara da cewa, babbar matsalar mata a wannan duniyar ita ce maza
Jaruma Inem Peter ta bayyana wani ra'ayi nata wanda ya janyo mata cece-kuce tare da maganganu daban-daban daga jama'a.
A ra'ayin jarumar, ta ce mata sun fi zama cikin tsananin farin ciki da walwala matukar basu tare da maza.
Jarumar ta wallafa wannan ra'ayin nata ne a shafinta na Instagram.
Kamar yadda ta wallafa: "Mata sun fi zama cikin matsanancin farin ciki matukar ba su tare da maza. Maza sune babbar matsalar mata a rayuwa."
Duk da dai babu wanda ya san takamaiman dalilin abinda yasa matashiyar jarumar masana'antar Nollywood din ta yi wannan wallafar, an dinga sukarta da maganganu.
KU KARANTA: Yadda masu garkuwa da mutane suka dinga lalata da mu kafin su sake mu, 'Yan matan Katsina
KU KARANTA: Bidiyo da hotunan ragargazar da soji suka yi wa 'yan bindiga yayin da suke kwashe shanu a Kaduna
A wani labari na daban, wata jarumar fina-finan Nollywood, Olive Utalor ta yi ikirarin mallakar duk wani abu da zai karkato da hankalin namiji a aure, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Jaruma Utalor ta fadi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da ita, inda ta tabbatar da yadda ta adana budurcinta har sai daren aurensu na farko.
Ta kara da cewa, ta tabbatar da yadda mijinta zai yi alfahari da ita, ta yadda ta adana budurcinta har aure.
A cewar jarumar; "Mijina zai yi alfahari da yadda na adana budurcina har sai da muka yi aure. Idan kun lura, ina da duk wasu abubuwa da za su dauki hankalin namiji.
"Duk da dai na fuskanci kalubale wurin adana budurcina har zuwa yanzun. Bana tsoron aure, saboda na daura dammarar fuskantar ko wanne irin kalubale.
"Idan na dage a kan abu, ina karkatar da duk hankalina ne a kan shi. Aure tarayya ce tsakanin mutane biyu masu kaunar juna, masu burin dagewa wurin fuskantar duk wani kalubale tare. Babu wani abinda zai dagamin hankali. Nasan aurena mai daurewa ne."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng