Tubabben dan Boko Haram ne ya bai wa 'yan ta'adda sirrin soji a harin Damboa, Ndume (Bidiyo)

Tubabben dan Boko Haram ne ya bai wa 'yan ta'adda sirrin soji a harin Damboa, Ndume (Bidiyo)

- Tubabbun 'yan Boko Haram ne suke cin amanar al'umma, cewar sanata Ali Ndume

- Sanatan ya ce su ne suke sanar wa da 'yan Boko Haram labarai sojoji

- Don haka, wajibi ne gwamnati ta dauki mataki a kansu

Sanata Ali Ndume ya zargi tubabbun 'yan Boko haram bai wa 'yan ta'addan bayanai a kan sojoji, musamman bayan ganin harin da suka kai Damboa kwanan nan.

Ndume, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar tarayya ta sojoji, ya sanar da hakan lokacin gabatar da kasafin sojoji a gaban kwamitin, ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ndume ya yi amfani da damar, inda yace wajibi ne gwamnatin tarayya ta soke shirin taimakonsu.

A cewarsa ba za a cigaba da fifitasu ba a kan sauran al'umma ba, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Ya bayar da misalin yadda 'yan Boko Haram suka je kauyensu, suka kwashi dattawa masu shekaru a kalla 60, suka yi musu yankan rago, saboda rashin imani.

Ya bukaci gwamnati da ta daina taimakon tubabbun 'yan Boko Haram domin komawa ruwa suke.

KU KARANTA: A karon farko, Tinubu ya magantu a kan daina biyan tsoffin gwamnonin Legas fansho

Tubabben dan Boko Haram ne ya bai wa 'yan ta'adda sirrin soji a harin Damboa, Ndume (Bidiyo)
Tubabben dan Boko Haram ne ya bai wa 'yan ta'adda sirrin soji a harin Damboa, Ndume (Bidiyo). Hoto daga @Lindaikeji
Asali: UGC

KU KARANTA: Tubabben Boko Haram ne ya halaka kanal din soja, Sanata Ndume

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya taya gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, murna a kan shirinsa na dakatar da ba wa gwamnoni da mataimakansu fansho, a matsayin matakan dakile almubazzaranci.

A wata wallafa da Tinubu yayi a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Laraba, ya ce: "Ina taya Gwamna Sanwo-Olu murna a kan kasafin da ya tsara, wanda dama hakan yayi daidai. Wannan kasafin zai taimaki mutanen jihar Legas, sannan zai taimaka wurin bunkasa jihar."

"Ina so in shawarci gwamnan da yayi gaggawar dakile fanshon gwamnoni da mataimakansu," cewar Tinubu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: