Saurayi ya halaka abokin takararsa wurin neman soyayyar budurwa a Bauchi

Saurayi ya halaka abokin takararsa wurin neman soyayyar budurwa a Bauchi

- Hukumar 'yan sandan jihar Bauchi sun kama wani saurayi mai shekaru 18 da laifin kashe wani a kan budurwa

- Al'amarin ya faru ne a ranar 11 ga watan Nuwamban 2020, da misalin karfe 9:45 na dare

- Duk da dai saurayin ya amsa laifinsa, amma ya sanar da hukuma abokansa 2 da suke da hannu a kan kisan

Hukumar 'yan sandan jihar Bauchi, sun kama wani saurayi mai shekaru 18, bisa zargin yanka wani saurayi a kan budurwa, shafin Linda Ikeji ya wallafa hakan.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Ahmed Wakil, ya sanar da hakan a wata takarda da ya saki a kan lamarin.

"A ranar 11 ga watan Nuwamba 2020, da misalin karfe 9:45 na dare, wani mutumin kirki ya kira mu inda yake shaida mana cewa an kashe wani Hamza Usman, mai shekaru 23 a Anguwar Mahaukata, a jihar Bauchi.

" Ya je hira wurin budurwarsa Ramlat Shehu (Ba sunanta na asali ba), mai shekaru 15. Wani Kabiru Ahmed da ke Karofi mai shekaru 18 ya soka masa wuka a kirji.

"Sakamakon yadda jini yayi ta zuba ne a daukeshi aka kai shi asibiti, inda likita ya tabbatar da cewa ya rasu.

"Bayan an sanar da hukumar 'yan sanda, wasu 'yan sanda sun je wurin da lamarin ya faru, inda suka damki Kabiru Ahmed, wanda ake zargin ya yi kisan," cewar Wakil.

A cewarsa, wanda ake zargin, ya amsa laifinsa, sannan ya ce wani Abdul (Walplay) da Waleed (Bandi), su ne suka taya shi.

Wakil ya ce yanzu haka ana kokarin kamo wadanda suka taya shi, sannan an mayar da al'amarin zuwa sashin bincike na manyan laifuka.

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan Dino Melaye yana kwasar rawa a hamada ya janyo cece-kuce

Saurayi ya halaka abokin takararsa wurin neman soyayyar budurwa a Bauchi
Saurayi ya halaka abokin takararsa wurin neman soyayyar budurwa a Bauchi. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tubabben dan Boko Haram ne ya bai wa 'yan ta'adda sirrin soji a harin Damboa, Ndume (Bidiyo)

A wani labari na daban, kotun majistare da ke Osogbo, jihar Osun, ta yanke wa wasu mata 2, Suliyat Tajudeen da Ayomide Abdulazeez, hukuncin dauri a gidan yari bisa laifin yunkurin kashe gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, da sunan zanga-zangar EndSARS.

An yanke musu hukunci bisa laifuka da dama, ciki har da yunkurin kisa, makirci, lalata dukiyoyi da barna.

Dan sanda mai gabatar da kara, John Idoko ya ce wadanda ake zargi, masu shekaru a kalla 20, sun yi fashi da sata a Osun Mall da yake a Osogbo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel