Kayatattun hotunan bikin dan Tambuwal, ministoci, gwamnoni da masu hannu da shuni sun halarta
- Masu iya magana sun ce kwarya ta bi kwarya, idan ta hau akushi kuwa sam bata moriya, an daura wani gagarumin aure a jihar Kebbi
- A ranar Asabar, an daura auren dan gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da diyar Sanata Umar Tafida na jihar Kebbi
- Bikin da manyan mutane masu fadi a ji a fadin Najeriya irin Abubakar Malami, Abubakar Bagudu, Bala Mohammed da sauransu suka samu damar halarta
An daura auren Najib Aminu Waziri, dan Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto, da Amina Umar Tafida, diyar Sanata Umar Tafida, Tafidan Argungu.
An daura auren ne a Argungu, jihar Kebbi, inda iyalan guda biyu da manyan mutane suka samu damar halarta, The Cable ta wallafa.
Cikin manyan mutanen da suka halarci bikin sun hada da Maigari Dingyadi, Ministan harkokin 'yan sanda, wanda ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari, Abubakar Malami, Antoni janar na gwamnatin tarayya kuma ministan shari'a da Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu.
Sauran wadanda suka halarta sun hada da Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, Garba Shehu, hadimin Buhari na musamman a kan harkokin yada labarai, Musa Haro, hadimin gwamnatin tarayya na musamman da Sheikh Abdullahi Bala Lau, Babban malamin musulunci.
Garba yayi wata wallafa a shafinsa na Twitter, inda yace: "Shugaban kasa ya amsa gayyatar da aka yi masa ta auren dan gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal."
Garba ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci ma'auratan da su kasance masu addu'a sannan su girmama juna.
"Ina shawartarku da ku kasance masu rike wa juna amana da kaunar juna," kamar yadda Garba yace shugaban kasa ya ce.
KU KARANTA: Bidiyo da hotunan Dino Melaye yana kwasar rawa a hamada ya janyo cece-kuce
KU KARANTA: Kotu ta bukaci a garkame mata wasu mutum 2 da suka yi yunkurin kashe Gwamna
A wani labari na daban, KADRIS ta ce za ta fara amsar N1000 don cigaban jihar na 2021 daga hannun duk wanda ya mallaki hankalin kansa, kuma mazaunin jihar Kaduna. Hakan zai cigaba ne duk shekara, Daily Nigerian ta ruwaito.
Shugaban hukumar, Dr Zaid Abubakar ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi a Kaduna, inda yace daga shekarar 2021, duk wani mai hankalin kansa da yake zaune a jihar wajibi ne ya biya wannan harajin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng